#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Posts

Showing posts from 2023

Juma'a 23, Yuni, 2023

Juma'a 23, Yuni, 2023

Saudiyya ta samar da motoci marasa matuƙa don jigilar mahajjata

Saudiyya za ta ƙaddamar da motoci marasa matuƙa masu amfani da lantarki, da za su yi jigilar mahajja a aikin hajjin bana. Hukumar kula da sufurin ƙasar ta ce ta ɗauki matakin ne domin zamanantar da kuma sauƙaƙa harkar sufuri a ƙasar. Matakin na daga cikin yunƙurin da hukumomin ƙasar ke yi don faɗaɗa harkokin sufuri musamman a lokacin aikin hajjin bana. Sabbin motocin masu sarrafa kansu na ɗauke da kyamarori da wasu abubuwa da za su sanya su yin aiki da kansu ba tare da wata matsala ba. Motocin kan tattara bayanai a lokacin da suke aiki, tare da yin nazari a kan bayanan, domin ɗaukar mataki. Manyan motocin waɗanda ke da kujeru 11, za su iya yin gudun kilomita 30 a cikin sa'a ɗaya, kuma batirinsu zai iya riƙe chaji na tswon sa'o'i 6.

Majalisar Kano ta tantance kwamishinoni 17 a cikin 19 da gwamna ya aike mata

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da mutum 17 daga cikin sunaye 19 da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin amincewa da naɗinsu a matsayin kwamishinoni a jihar. Majalisar ta amince da sunayen ne a zamanta na ranar Alhamis, ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jihar Isam'il Falgore. An dai amince da mutum 17 daga cikin mutum 19 da gwamnan jihar ya aike wa majalisar, in ban da Sheikh Tijjani Auwal da Hajiya Aisha Soji, waɗanda ba su halarci majalisar ba, sakamakon tafiyarsu aikin Hajji. Bayan kammala tantance kwamshinonin, a yanzu hankali ya koma kan ma'aikatun da kwamshinonin za su jagoranta bayan an rantsar da su.

Jami'an tsaro na farautar 'yan bindigar da suka kashe mutum 15 a Plateau

Hukumomin jihar Plateau da ke tsakiyar Najeriya sun ce jami'an tsaro na neman 'yan bindigar da suka kai hare-hare kan wasu garuruwa biyu, tare da kashe a ƙalla mutum 15 a jihar. Rahotonni na cewa 'yan bindigar sun kashe wasu manoma shida a yankin Riyom, yayin da waso 10 suka rasa rayukansu a yankin Mangu ranar Talata. Maharan sun ƙaddamar da hari kan garuruwan biyu inda suka kashe mutane tare da cinna wuta kan gidaje masu yawa. Mai magana da yawun gwamnan jihar Mista Gyan Bere ya shaida wa BBC cewa an shirya tawagar jami'an tsaro da ta ƙunshi sojoji da 'yan sanda domin kare garuruwan tare da farauto maharan. Ya ƙara da cewa gwamnan jihar ya gaji irin waɗannna hare-hare ne daga tsohuwar gwamnatin jihar. ''Gwamna na ganawa da shugabannin tsaro da jagororin al'umma domin magance matsalar da ake ciki, da kuma maido da zaman lafiya a faɗin jihar'', in ji shi. Mista Bere ya ce gwamnatin jihar ba ta kai ga gano waɗanda ke kai hare-ha

Tinubu ya hallara a wurin taron harkokin kuɗi a Paris

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa dakin taron da za a gudanar da babban taron harkar kuɗaɗe da tallafawa ƙasashe masu rauni, da za a gudanar a birnin Paris. Shugaban ya samu tarbar ministar harkokin ƙasashen wajen Faransa da nahiyar Turai Catherine Colonna. Taron shi ne na farko da shugaban na Najeriya ke halarta tun bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasar ranar 29 ga watan mayun da ya gabata.

Atiku na gabatar da shaidu a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa

Kotun sauraron ƙararraƙin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya ta ci gaba da zaman saurarorin ƙorafin jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar. A baya dai kotun ta ɗage zaman sauraron ƙararrakin zuwa yau Alhamis domin bai wa jam'iyyar damar gabatar da shaidunta. Jam'iyyar PDP da ɗan takarar tata Atiku Abubukar sun shigar da ƙara a gaban kotun domin kalubalantar nasarar da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC. Hukumar zaɓen ƙasar INEC ce ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu. Matakin da jam'iyyun adawa ciki har da PDP da LP suka ce ba su gamsu da shi ba. Lamarin da ya sa jam'iyun da 'yan takararsu suka garzaya kotun suna neman ta soke zaɓen da ya bai wa Tinubu nasara a zaɓen.

Muhuwi zai binciki Ganduje abubuwa hudu

Shugaban hukumar sauraron ƙorafe-ƙorafen al'umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano watau PCACC, Barista Muhuyi Magaji ya ce zai gudanar da wasu jerin bincike a kan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da gwamnatinsa. Daya daga cikin binciken da shugaban na yaki da rashawa a Kano yace zai mayar da hankali a kai shi ne binciken 'bidiyon dala'. A ranar Laraba ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi kan muƙaminsa nasa, bayan korarsa da tsohuwar gwamnatin jihar ta yi bisa dalilin cewa akwai shakku kan yanayin tafiyar da ayyukansa. Sai dai kwana ɗaya bayan mayar da shi kan muƙamin, shugaban na PCACC ya shaida wa BBC cewar akwai wasu jerin zarge-zarge a kan gwamnatin Ganduje, waɗanda yake shirin buɗe bincike a kansu. Ya ce "Za mu ɗora daga inda muka tsaya, dama akwai wasu bincike-bincike da muke yi wadanda daga baya wasu suke ganin ba za su yadda a ci gaba da yi ba saboda ya shafe su." Lamarin ya fara tay

An ga watan Sallah a Najeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya. Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce ganin jinjirin watan da aka yi a a kasar ya sanya ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1444. Kwamitin tantance ganin wata karkashin jagorancin Maigirma Wazirin Sakkwato Farfesa. Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan a bana. Cikin sanarwar da ya yi Sarkin Musulmi ya ce "mun samu bayanai daga wurare daban-daban a Najeriya kuma mun zauna da masana domin tabbatar da ingancin waɗannan bayanan gabanin mu sanar da al'umma cewa an ga watan. Domin haka gobe Juma'a 21 ga watan Afrilu 2023 ita ce 1 ga watan Shawwal 1444," in ji Sarkin Musulmi. Ya yi kira ga sauran musulmin ƙasar da su ajiye azumi domin an ga wata, su kuma yi shirin zuwa masallaci domin halartar Sallar Idi a wurare daban-daban. Akasarin Musulmai a fadin duniya dai sun tashi da Azumin watan Ramadan ra

Sallah sai ranar Asabar a Iran

Ofishin Jagoran addinin na Iran Ali Khamenei ya sanar da cewa ba a ga jaririn watan Shawwal ba a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilun 2023, don haka watan Ramadan zai ƙare ranar Juma'a 21 ga watan Afrikun, Asabar ta zama sallah 1 gawatan Shawwal. A cewar rahotanni kimanin ƙungiyoyi 100 aka aika yankuna mabambanta domin aikin ganin jaririn watan na Shawwal. Rahotannin sun ce wasu daga cikin waɗanda suka yi aikin duba watan a ƙauyen Qom yanayin duhun gari ne ya hana su ganin shi.

An ga watan Sallah a Saudiyya

Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin watan Shawwal na sallah a ranar Alhamis 20 ga watan Afrilun 2023. An ga watan ne a yankin Tumair na Saudiyya kamar yadda kwamitin duban wata na yankin ya bayyana, hakan na nufin Saudiyya ta kammala azumin Ramadan 29. Gobe Juma'a 21 ga watan Afrilu zai zama 1 ga watan Shawwal.

Juma'a 7 ga Afrilu, 2023

Juma'a 7 ga Afrilu, 2023

Kalaman Peter Obi sun yamutsa hazo a siyasar NajeriyaA Najeriya

Cacar-baki ta kaure tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar da na jam'iyyar Labour mai adawa. Lamarin na zuwa ne, tun bayan jin wata tattaunawar wayar salula tsakanin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi da Bishop David Oyedepo, wani babban limamin Kirista na majami'ar Living Faith Church. A ƙarshen mako ne, wata jaridar intanet mai suna People Gazette ta wallafa wannan murya da aka kwarmata, tsakanin Peter Obi da babban limamin Kiristan, Bishop David Oyedepo. Wannan ya janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta a ƙasar. Musamman ma yadda aka ji ɗan takarar yana roƙon malamin ya taimaka wajen nema masa goyon bayan mabiya addinin kirista da ke shiyyar kudu maso yammacin Najeriya da kuma shiyyar arewa ta tsakiyar ƙasar. Ya dai alaƙanta siyasar da takararsa, tamkar wata fafutukar yaƙi na addini, har ma ya tattabar wa limamin Kiristan da cewa ba za su yi da-na-sanin goya masa baya ba. `Yan jam`iyya

Kada Ku Sake Bai Wa Gwamnati Mai Barin Gado Bashi —Abba

Zababben gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shawarci bankuna da su daina bai wa gwamnati mai barin gado bashi. Wannan dai na zuwa ne bayan shawarar da ya bai wa masu gine-gine a filayen gwamnati, makarantu, makabartu da sauransu. Yusuf ya bayar da wannan shawara kan gine-gine ba bisa ka’ida ba a wurare jama’a. Sai dai kuma gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta ce ya daina zumudi ya bari a rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu. Amma a cikin wata shawara da ya sake barwa da ke kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan mai jiran gado, Sanusi Bature Dawakin Tofa, Abba ya jadadda cewar cewa shawarar ta zama dole. Sanarwar ta ce: “Daga ranar 18 ga watan Maris zuwa 29 ga Mayu, babu wani mai ba da lamuni (na gida ko na waje) da zai amince da bayar da rance ga gwamnatin Jihar Kano ba tare da amincewar gwamnati mai zuwa ba. “Duk masu ba da rancen kudi ga Gwamnatin Jihar Kano su lura cewa gwamnati mai barin gado na cin bashi ba g

Obasanjo ya bukaci kotun Birtaniya ta sassauta wa Ekweremadu hukunci

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya rubuta wa jami'an kotu a Birtaniya , inda yake bukatar a yi sassauci lokacin yanke wa sanatan Najeriya Ike Ekweremadu da matarsa hukunci bayan kama su da laifin 'safarar sassan jikin ɗan bil'adama.' A watan da ya gabata ne kotu ta samu sanata Ike Ekweremadu mai shekara 60 da matarsa Beatrice da kuma wani likita Dr Obinna Obeta da laifin ɗaukar wani matashi ɗan shekara 21 daga Legas zuwa Birtaniya domin cire ƙodarsa, domin a bai wa ƴarsa Ekweremadu, mai suna Sonia, mai shekara 25. A wasikar da Obasanjo ya rubuta, ya ce abin da ma'auratan suka yi ba daidai ba ne kuma babu wata al'umma da za ta lamunci aikata hakan. Sai dai ya bukaci kotun da ta duba lamarin ƴar sanatan wadda lafiyarta ke cikin haɗari da kuma ke son agajin lafiya na gaggawa domin sassauta masa. Obasanjo ya kuma faɗa wa kotun cewa ta duba ɗabi'u masu kyau da Ekweremadu ke da su a lokacin yanke masa hukunci. Sai dai babu tabbacin cewa ko w

Zan yi nesa da Abuja idan na sauka daga mulki - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai koma mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, idan ya miƙa ragamar mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa a ranar 29 ga watan Mayu. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, ya ce Buhari ya faɗi haka ne jiya Laraba lokacin da ya karɓi bakuncin Jakadiyar Birtaniya a Najeriya mai barin gado, Catriona Wendy Laing. Buhari ya yaba wa ƙasar Birtaniya kan tallafa wa Najeriya a ɓangarori da dama, musamman ma wajen sake gina yankin arewa maso gabas da ayyukan ƴan tayar da ƙayar-baya ya ɗaiɗaita. Ya ce Birtaniya ta kasance gida ga ƴan Najeriya da dama, inda ya ce dangataƙar ƙasashen biyu za ta ci gaba da wanzuwa. Tun da farko, Jakadiyar Birtaniyar ta ce ba ta jin daɗi barin Najeriya da za ta yi, musamman ma ganin cewa ta saba da abubuwa da dama a ƙasar, kamar al'adu da raye-raye da kuma wakokin ƴan ƙasar masu daɗi. Ta ce ta ji daɗin kasancewarta a Najeriya, inda ta ce ta ziyarci jihohi sama da 20. Ta ce "na

Yan mata 20,000 da aka aurar bara sun haifi jarirai 10,000 a Iran

'Yan mata fiye da 20,000 ne 'yan shekara 15, aka yi wa aure a cikin wata taran da ya gabata a ƙasar Iran, a cewar alƙaluman Cibiyar Ƙididdiga ta Ƙasar. A cewar alƙaluma da jaridar intanet ta Etemad ta wallafa, an kuma samu "sakin aure 179 a cikin 'yan matan 'yan ƙasa da shekara 15". Akwai 'yan mata 'yan ƙasa da shekara 15 da suka haifi jarirai 1,085. Cibiyar Ƙididdigar ta wallafa wannan rahoto ne a kan halin rayuwar zamantakewa da ta al'adar al'ummar Iran a cikin watanni ukun farkon shekara. A cewar dokokin kula da hulɗar jama'a na Iran, shekarun aure ga 'ya mace suna farawa ne daga 13, maza kuma daga shekara 15. Haka zalika, ana iya aurar da mutum wanda shekarunsa ba su cika ƙa'ida ba, bisa doka amma da sharaɗin yardar mahaifi ko wani mai kula da shi sannan sai kotu ta amince. Yunƙurin canza shekarun aure a majalisar dokokin Iran yana da dogon tarihi a ƙasar.

Kafa gwamnatin rikon kwarya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya ne — Hedikwatar Tsaro

Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana kiran gwamnatin wucin gadi da wasu mutane ke yi a kasar a matsayin abin takaici da kuma saba wa kundin tsarin mulkin kasar. Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Musa Danmadami, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a taron mako biyu kan ayyukan sojoji a fadin kasar nan ranar Alhamis a Abuja. Danmadami ya ce masu kira da a kafa gwamnatin rikon kwarya suna kokarin yin barna ne kawai, ya kara da cewa kundin tsarin mulkin kasar bai tanadar da gwamnatin wucin gadi ta kasa ba. Ya ce: “Akan batun gwamnatin wucin gadi, abin takaici ne. “An gudanar da zabe kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, da aka bawa izini ta sanar da zababben shugaban kasa. “Ba alhakinmu ba ne mu yi magana a kan wannan batu amma na san cewa an yi kira da yawa daga fadar shugaban kasa cewa babu wani abu kamar gwamnatin wucin gadi ta kasa. "Don haka ina tsammanin mutane suna ƙoƙarin yin ɓarna ne kawai. Ya saba

‘Yan Arewa na shirin maye gurbin Tinubu da Shettima – Naja’atu Mohammed

Naja’atu Mohammed, ta bayyana shirin da ‘yan Arewa ke yi na maye gurbin dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da abokin takararsa, Kashim Shettima. Naja’atu ta yi ikirarin cewa wasu ’yan Arewa ne ke kira ga Tinubu ya ci gaba da cewa Shettima zai maye gurbinsa idan lafiyarsa ta tabarbare kuma ya gaza. Da take magana da jaridar ThisDay, Naja’atu ta ce: “Suna so ne kawai su tura shi ya zama shugaban kasa. Ko da bai dace da sha’awarsa ba.” “Wasu mutane daga Maiduguri sun kira ni yau suna tambayar, ‘Hajiya, me ya sa kika yi haka? Yanzu kina sukar kudirinmu. Danmu zai zama shugaban kasa, amma kina magana irin wannan? Bayan haka ma, yanzu dubi Tinubu; ba zai iya ba. Mu duka don Kashim muke yi. Ba ki kyautata mana ba.” Naja’atu ta kuma yi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai damu da tattalin arziki, tsaro, ko kuma wanda zai gaje shi a matsayin shugaban kasa ba. Ta bayyana cewa, duk da bayanan da aka samu daga dukkan hukumomin tsaro, shugaban bai damu da

Cire tallafin man fetur: Bankin Duniya ya baiwa FG $800m don bayar da tallafi

Babban Bankin Duniya ya ba wa gwamnatin Najeriya dala miliyan 800 domin ta samar da wani tsari mai inganci ga ‘yan kasarta, kafin a cire tallafin man fetur nan da watan Yunin 2023. Ministan kudi, kasafin kudi da kuma Tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa (FEC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta. A cewar Ahmed, gwamnatin Najeriya ta kuduri aniyar kawo karshen tallafin man fetur nan da watan Yuni, don haka ta fara wani yunkuri na rage wa ‘yan kasar damuwa. Ta yi nuni da cewa, tuni aka samu kyakkyawar alaka da sabuwar majalisar rikon kwarya ta shugaban kasa (PTC) da kuma gwamnati mai zuwa, da nufin tafiyar da shirin. "Mun samu makudan kudade da suka kai dala miliyan 800 daga bankin duniya domin tafiyar da ayyukan jin kai, kuma muna tunkarar gidaje kusan miliyan 10 ko kuma 'yan Najeriya miliyan 50 masu rauni a matakin farko." In ji Ministan yayin da t

Hukumar NBC a Nijeriya ta ci tarar gidan talabijin na Channels naira miliyan biyar

Hukumar da ke kula da gidajen rediyo da talabijin ta Nijeriya NBC ta maka wa gidan talabijin na Channels a kasar tarar naira miliyan biyar kan saba ka’idojin watsa labarai. Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa NBC ta aika wa gidan talabijin din takardar tarar ne a sakamakon wani shiri na siyasa da aka yi da mataimakin dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar Labour Dr Datti Baba-Ahmed. Takardar mai taken “Hirar tunzurarwa, saka takunkumi”, na dauke da sa hannun shugaban hukumar wato Balarabe Shehu Ilelah. “Hukumar NBC ta kalli wata tattaunawa da aka yi kai tsaye da mataimakin dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar Labour, Dakta Datti Baba-Ahmed, wadda jagoran shirin Politics Today, Seun Okinbaloye ya jagoranta a ranar Laraba, 22 ga watan Maris. “Dakta Baba-Ahmed ya bayana cewa za a saba wa kundin tsarin mulki idan aka rantsar da zababben shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, saboda kurakuran zabe,” in ji Ilelah a takardar. Ya bayyana cewa wannan t

Saudiyya ta ƙwace tan biyar na naman kaji da ya lalace

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Saudiyya (SFDA) ta ƙwace tan biyar na naman kajin da ya lallace a wani gidan ajiye kayyakin abinci da ke birnin Riyadh. Hukumar ta tabbatar da cewa gidan ajiyar kayan abincin ya saɓa wa ƙa'idoji masu yaw, cikin har da yin ƙarya sayar da kayayyakin da suka lalace, inda ake sake wa naman kajin mazubi tare da sanya musu sabbin kwanan watan lalacewa. Haka kuma hukumar ta ce gidan ajiyar ya saɓa wa dokokin lafiya, da amfani da ma'aikatan da ba su da takardun shaidar karatun lafiya. SFDA ta kuma rufe gidan ajiyar tare da lalata duk kayyakin da ta ƙwace. Hukumar ta ce ta gudanar da wannan aiki ne tare da hadin gwiwwar hukumar gudanarwar birnin Riyadh da ma'aikatar kasuwanci da ma'aikatar walwala da ci gaba jama'a da hukumar zakka da haraji ta ƙasar tare kuma da hukumar fasa ƙwauri ta ƙasar. Haka kuma hukumar ta yi kira ga kwastomomi da su kai rahoton duk wani shago ko kamfanin da ya sayar musu da kayayyakin da suka lal

Amurka ta ƙwace $53m daga hannun Diezani bayan kama ta da laifi

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta cimma matsaya kan wasu shari'u biyu da suka buƙaci ƙwace wasu manyan kadarori na alfarma da aka samar da su a ƙasar ta hanyar laifukan almundahanar kuɗaɗe. Wasu takardu daga ma'aikatar shari'ar ƙasar sun nuna cewa batun ya shafi tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke da wasu abokan kasuwancinta biyu Kolawole Akanni Aluko da Olajide Omokore. Da wannan mataki a yanzu ma'aikatar shari'ar ƙasar ta ce ta ƙwace kuɗin da ya kai dala miliyan 53.1, ƙimar kuɗin kadarorin idan aka sayar da su. Takardun kotun sun nuna cewa daga shekarar 2011 zuwa 2015 Diezani wadda a lokacin take ministar man fetur a Najeriya ta karɓi cin hanci daga abokan kasuwancinta. Wadda ita kuma Diezani ta riƙa bai wa kamfanoninsu manyan kwangilolin man fetur. Ma'aikatar shari'ar Amurkan ta ce an yi amfani da kuɗaden da aka biya a matsayin cin hancin da yawansu ya kai sama da dala miliyan 100, wajen sayan manyan kada

Zargin kafa gwamnatin riƙo a Najeriya abin fargaba ne - Jam'iyyu

Kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyun Najeriya ya ce zargin kafa gwamntin riƙo a ƙasar, babban abin tayar da hankali ne da cusa fargaba. Shugaban kwamitin, Engr Yabagi Sani ya ce “Ba ma mu ‘yan siyasa ba kaɗai ba, duk wanda ke kishin Najeriya, yake da kishin ci gaban Najeriya, yake kishin dimokraɗiyya ta kafu a Najeriya. Idan aka dubi matsayin Najeriya ba ma a Afirka kaɗai ba, a duniya gaba ɗaya, abin da DSS ta fito da shi, abu ne na fargaba”. Engr. Sani na mayar da martani ne kan zargin da DSS ta yi cewar wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a ƙasar na shirya maƙarƙashiyar kafa gwamnatin riƙon ƙwarya don hana rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasa nan gaba cikin wata Mayu. Ya ce a ganinsa, abin da ya janyo kitsa irin wannan maƙarƙashiya da ake zargi, shi ne rashin gamsuwar da mai yiwuwa wasu ‘yan siyasa ke da ita kan zaɓukan 2023 da kammala a baya-bayan nan. "Lallai waɗanda ba su gamsu da abin da hukumar zaɓe ta fito da shi ba ne, mai yiwuwa cikinsu ne aka samu waɗan

Gobara ta tashi a kasuwar kayayyakin gyaran mota da ke jihar Legas

Getty ImagesCopyright: Getty Images Wata gobara ta tashi a kasuwar kayayyakin gyaran mota da na laturoni ta Olowu da ke jihar Legas. Gobarar ta tashi a kasuwar ne a daren da ya gabata, sai dai gobarar ta yi ɓarna kafin jami'an kashe gobara su kai ɗauki. Sai dai ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma wasu mutane na danganta tashinta ne da barin wutar lantarki a kunne yayin da dama kuma ke cewa tana da nasaba da siyasa. Wannan dai ita ce gobara ta uku cikin makwanni uku da aka samu tashinta a birnin Legas.

Ƴar fafutukar Saudiyya Salma al-Shebab ta shiga yajin cin abinci

Yar fafutukar nan ta kasar Saudiyya Salma al-Shehab, wadda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru 27 sakamakon bayanan da ta yaɗa a shafin Twitter, ta shiga yajin cin abinci. Kungiyar kare hakkin ɗan adam ta ALQST ta ce Mis al-Shehab da wasu mata bakwai da aka tsare a Saudiyyar, sun fara yajin cin abinci mako guda da ya gabata. Salma al-Shehab wadda ke karatun digirin digir-gir a ƙasar Birtaniya, an kamata ne a lokacin da ta koma gida hutu shekaru biyu da suka gabata. Ana tuhumarta ne da laifin taimaka wa masu sukar manufofin gwamnatin Saudiyya da ke neman tayar da zaune tsaye ta hanyar wallafa bayanai babu kakkautawa a shafin twita. Tun da farko dai an yanke mata hukuncin ɗaurin shekara shida, inda daga bisani aka mayar da shi shekaru 34, sannan aka rage zuwa shekaru 27.

Ukraine ta ce: "Duniya za ta yi bankwana da zaman lafiya da Rasha ta samu jagorancin MDD"

Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya bayyana jagorancin Rasha a MDD da cewa tamkar wata mummunar tsokana ce. Rasha dai ita ce ake sa ran zata karbi shugabancin karba-karba na MDD na kwanaki 30 a ranar Asabar. Sai dai Mista Kuleba yace, Rasha ta jagoranci laifukan yaki, kuma ta shirya yaki na salon mulkin mallaka kan Ukraine. Ya ce duniya zata yi bankwana da zaman lafiya, muddin Rasha ta samu bakin magana. Rasha dai na daga cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na MDD.

Martanin jam'iyyu kan kammala zabuka

A Najeriya, tuni wasu `yan takara da ke dakon a kammala zabensu suka yi maraba da sanarwar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasar INEC, wadda ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu mai zuwa don kammala zaben gwamnoni da na`yan majalisun dokoki a wasu sassan kasar. Sanarwa INEC din ta kawo karshen dogon zaman jiran da al`umomin yankunan da zaben ya shafa da kuma `yan takara ke yi. Jihar Adamawa da Kebbi su ne jihohi biyu rak da ba a kammala zaben gwamna ba a Najeriyar. Tsohon ministan lafiya da harkokin wajen Najeriya kuma jigo a kwamitin yakin neman zaben gwamna Fintiri na jam’iyyar PDP a Adamawa, Dr Idi Hong, ya shaida wa BBC cewa, tsayar da ranar sake zaben za ta ba su damar sake shiri har su sake zuwa wuraren da aka soke zabensu don sake yada manufofinsu. Ya ce, “ Dama mu jam’iyyar PDP masu bin doka ne don haka za mu jira ranar da aka tsayar don sake zaben nan, idan aka yi zaben nan za a gane bambanci.” A jihar Kebbi ma zaben gwamnan da aka yi a zagayen farko, kamar yadda hukumar za

INEC ta sanar da ranar sake zabe a Kebbi da Adamawa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta bayyana ranar da za a sake gudanar da zabukan jihohin Kebbi da Adamawa. Babban Sakataren Yada Labarai na INEC, Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi ne, ya bayyana hakan a birnin Abuja. Ya ce za a gudanar da zabukan gwamnoni da na wasu ‘yan majalisar tarayya da na jihohi a rana guda. Yayin taron da ta gudanar a ranar Litinin, INEC ta yanke shawarar cewa za a gudanar da dukkanin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi a ranar Asabar, 15 ga Afrilu, 2023,” in ji Oyekanmi. Ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da cikakken bayani kan yadda zaben zai gudana a hukumance. Rahotanni sun nuna cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi na ranar 18 ga watan Maris, an soke zabukan wasu mazabun, abin da ya sanya INEC ayyana sakamakon wasu jihohin a matsayin wadanda ba su kammala ba

PDP ta maye gurbin Iyioricha Ayu bayan dakatar da shi

Iyioricha Ayu lokacin da ya lashe zaben shugabancin jam'iyyar ta PDP. Iyioricha Ayu lokacin da ya lashe zaben shugabancin jam'iyyar ta PDP. Kwamitin ayyuka nababbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ya maye gurbin shugaban jam’iyyar Sanata Iyioricha Ayu. A wani taron gaggawa da jam’iyyar ta yi a ranar Talata, kwamitin ya amince da umarnin babbar kotun jihar Benue, wadda ta haramta wa Ayu bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar. Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce bayan yin nazari da kyau da umarnin kotu da kuma bin sashe na 45 (2) na kundin tsarin mulkin PDP da aka yi wa gyara a 2017, kwamitin ya yanke shawarar cewa Mataimakin Shugaban shiyyar Arewa, Ambasada Umar Ilyya Damagum shine zai rike shugabancin jam’iyyar. Rikicin jam’iyyar bayan zaben kasar, ya dauki wani sabon salo a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da masu ruwa da tsaki na gundumar Igyorov a karamar huk

Yadda za ku guje wa galabaita saboda tsananin zafi a lokacin azumi

Hukumar lura da yanayi ta Najeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa za a fuskanci tsananin zafi a wasu jihohin Najeriya. A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, NiMet ta ce yanayin wanda ake sa ran ya fara daga Litinin zai iya haura digiri 40 a ma'aunin salshiyas. Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da Kwara. Sai kuma birnin Tarayya Abuja da Nasarawa da Benue da Bauchi da Gombe da kuma Borno. Nimet ta ce za a fuskanci yanayin na zafin rana ne a tsawon kwanaki biyu masu zuwa. Nimet ta ce jihohin da makin zai haura 40 sun haɗa da wasu sassan Sokoto da Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa. Hukumar ta sharwarci mutane da ke zaune a jihohin da abin zai shafa, da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin. Sai dai lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da al'umma musulmi ke gudanar da azumin Ramadana a Najeriyar da ma sauran ƙasashen duniya.

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano

Canjin kuɗi : Har yanzu jama'a na shan baƙar wahala a Najeriya

Jama'a a Najeriya na ci gaba da fuskantar wahala ta samun takardun kudi a bankuna duk da alkawarin da babban bankin kasar ya yi cewa kudaden za su wadata daga ranar Alhamis 23 ga watan nan na Maris. A ranar Laraba ne babban bankin, ya umurci bankuna da su je rassan CBN na jihohi su karbi tsofaffin takardun kudaden da suka ajiye don saukaka wa jama’a matsalar karancin kudin da ake fama da ita. Ana ganin babban bankin ya bayar da wannan sanarwa ne bayan da kungiyar kwadago ta kasar NLC ta yi barazanar mamaye dukkanin ofisoshin bankin da ke jihohi ciki har da Abuja domin tilasta wa gwamnati ta dauki matakin na saukaka wa jama'a halin da ake ciki. NLC ta ce daga mako mai zuwa ne za ta mamaye ofisoshin bankin domin hana su gudanar da ayyukansu. To sai dai a binciken da BBC ta yi daga rahotannin da ta samu daga wakilanta a wasu sassan kasar har yanzu al'amarin ba sauki ta yadda jama'a ba sa samun isassun kudin walau sababbi ko ma tsofaffin a cikin bankunan da ma

Sarkin Kano Aminu Ado ya taya Abba Kabir murnar zama gwamna

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga watan Maris. Cikin wata wasiƙa da ya aike da ita, Sarkin Kano ya ce ya fahimci mutane sun karɓi dimokradiyya hannu biyu-biyu, kuma abu mafi mahimmani shi ne yadda suka fito suka kaɗa kuri'unsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Gabanin haka shi ma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya aike da ta shi wasiƙar taya murna ga sabon zaɓaɓɓen gwamnan, wanda ya ce a madadinsa da iyalansa ya aika sakon. Sarkin Rano ma Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa ya aike da na shi saƙon tare da fatan Allah ya taya sabon shugaban riƙo da shugabancin mutanen Kano. Duka sarakunan sun miƙa godiya ga malaman addinai da shugabannin jama'a da suka riƙa wayar da kan al'umma, aka yi zaɓe lafiya aka gama lafiya.

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DA DUMI-DUMI: An ga watan azumin Ramadan a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na uku ya sanar da ganin jaririn watan Ramadan na shekarar 2023 a wasu sassan Najeriya. A jawabin da ya yi na sanarwar wanda aka sanya a shafin Tuwita na kwamitin ganin watan, Sarkin Musulmin ya ce an ga watan ne bayan samun rahotanni daga shugabannin addinin Musulunci da ke wasu jihohin ƙasar. Hakan na nufin ranar Alhamis 23 ga watan Maris din 2023 ne za ta kasance daya ga watan Ramadan.

Gwamnoni huɗu da zaɓe bai musu daɗi ba

An kammala zabukan shugaban ƙasa da na gwamnoni da kuma ƴan majalisar Dokoki na tarraya da kuma jihohi a fadin Najeriya. Zaben ya bar wadansu ƴan siyasa cike da murna yayin da wadansu ƴan siyasar suke cike da bakin ciki, saboda yadda sakamakon ya kasance. A waɗansu jihohin ƙasar an samu sauyi a jam’iyyar da ke mulki inda ƴan adawa suka samu nasara a yayin da a waɗansu kuma masu mulkin ne suka samu dama domin ci gaba da jan ragama. Bari mu duba jihohi huɗu da suka fi jan hankali, watau Kano da Zamfara da Sokoto da kuma Plateau. ‘Makomar Ganduje a Kano’ Tun bayan zaben shugaban ƙasa a jihar Kano inda jam’iyyar APC mai mulki ta sha kaye a hannun jam’iyyar adawa ta NNPP, alamu suka nuna cewa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje sai ya dage idan har yana son ɗan takarar APC, Nasiru Gawuna ya ci zabe. Amma bayan kammala zaɓen gwamna a ƙarshen mako, sai jam’iyyar NNPP ta kwace ragamar jihar inda hukumar zabe ta ƙasa INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwam

Jerin Gwamnoni Takwas da suka yi tazarce

ranar Asabar 18 ga watan Fabrairu aka gudanar da zaɓen gwamnoni da kuma na ƴan majalisun dokoki na jihohi a Najeriya. Yayin da aka sanar da sakamakon wasu jihohi, wasu kuma ana ci gaba da tattara sakamakon. Ga jerin gwamnoni da suka yi tazarce a kan kujerunsu a zaɓen da aka gudanar. Lagos Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe na jihar Legs, Professor Adenike Temidayo Oladiji ya bayyana gwamna ma ci Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya samu nasarar komawa kan mulki karo na biyu. Sanwo Olu ya samu nasara ne da ƙuri'u 762,134. Gombe A jihar Gombe ma, hukumar zaɓe ta hannun jami'ar tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar, Farfesa Maimuna Waziri ta ayyana Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya yi nasarar sake ɗarewa kan mulki da kuri'u 345,821. Kwara Hukumar zaɓe a jihar Kwara, ta ayyana gwaman mai ci AbdulRahman AbdulRazaq a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamna. AbdulRahman ya koma kan mulki ne bayan samun nasara a illahirin kananan hukumomi 16 na faɗin jih

YANZU-YANZU: Ƴan daba sun tarwatsa masu zaɓe a wasu sassan Najeriya

Rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriya na cewa ƴan daba sun tarwatsa masu zaɓe a sassan ƙasar. Kano: Wani hoto ya nuna yadda masu matasa da ake zargin ƴan daba ne sun tarwatsa kayan zaɓe, suka kuma kori jama'a a ƙaramar hukumar Rogo. Lamarin ya faru ne a a lokacin da ake zaɓen gwamnnoni da na ƴan majalisun dokoki. Lagos: Rahotanni daga kafofin sada zumunta da dama sun nuna cewa an samu tashin hankali a wasu rumfunan zaɓe a cibiyar kasuwancin ƙasar ta Najeriya. Wata tauraruwar fina-finan Nollywood Chioma Akpotha ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram inda ta yi zargin cewa wasu mutane sun kai mata hari da wuƙa. "Ban iya ma fito da waya ta ba lokacin da yaran nan suka zo, suka ringa dukan motata, suka fasa min madubin gefe na mota..." tana magana ne a lokacin da take barin rumfar zaɓen. Bayelsa: Rahotanni na cewa wasu ƴan daba sun kwace tare da lalata kayan zaɓen ɗan majalisar dokoki a rumfuna masu lamba 02 da 03 da 04 da kuma rumfa ta 05 a mazaɓa ta

YANZU-YANZU: An dakatar da kada kuri'a a rumfunan zabe tara a jihar Taraba

An an dakatar da kada kuri’a a rumfuna tara a mazabun Gyetta Aure da Asibiti na karamar hukumar Donga a jihar Taraba. Zanga-zanga ta barke a wasu sassan jihar yayin da masu kada kuri'a a yankin suka yi zargin cewa kuri'un na bogi ne da takardar sakamakon zabe. ICRI ta bayyana cewa masu kada kuri’a a unguwannin Gyetta Aure da Asibiti na karamar hukumar Donga a yankin Taraba ta Kudu na zanga-zangar nuna rashin amincewa da gano takardun zabe na bogi da kuma takardar sakamakon zabe. Rahotanni sun ce zanga-zangar ta dakatar da kada kuri'a a rumfunan zabe tara na gundumar. Da yake bayar da bayanin yadda lamarin ya faru, wani mai lura da zaben ya ce a yanzu masu kada kuri’a sun karaya wajen kada kuri’a kan gano takardun zabe da sakamakon bogi da ake zargi. An kuma bayyana cewa, a lokacin da ake gabatar da rahoton, an mayar da dukkan kayayyakin zaben zuwa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke unguwar.

DA DUMU-DUMI: 'Yan sanda sun kubutar da ma'aikatan INEC 17, a jahar Imo

Jami’an ‘yan sanda a jihar Imo sun ceto ma’aikatan wucin-gadi na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) guda goma sha bakwai a jihar Imo. Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi garkuwa da jami’an hukumar ta INEC da aka tura zuwa mazabu goma 19 a karamar hukumar Ideato ta Kudu, a kan hanyarsu ta zuwa wajen da za su yi aiki daban-daban. Sai dai an rawaito cewa ‘yan sandan sun yi gaggawar ceto su daga baya. Da yake magana da manema labarai a ranar Asabar, mai magana da yawun hukumar ta INEC na jihar, Dr. Chineye Chijioke-Osuji, ya tabbatar da ceto jami’an. Chijioke-Osuji, ya ce an ceto jami’an zaben ne ba tare da kayayyakin zabe ba da kuma na'urar (BVAS). Talla <img alt="" border="0" height="320" data-original-height="1080" data-original-width="720" src="https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEivgSeNsTUTVtamKB34OxjFNjFbQ62jitxQ9Qa6goEmd1V_iGeOJX1ECI04mlV67Pry7i5nP9DEcd35DIn

Zaben Gwamnoni- Mene ne mutane za su yi la’akari da su?

Abubuwan da mutane za su yi la’akari da su wajen zaɓen gwamnoni sun banbanta daga wata jiha zuwa wata. Misali, matsalar cunkoson ababen hawa da ta muhalli da hanyoyin sufuri su ne manyan matsalolin da ke addabar jihar Legas. Jihohi irin su Kaduna, da Katsina da Zamfara kuwa na fama da matsalar tsaro. Akwai kuma jihohi irin Kano da Sokoto, da Bauchi waɗanda ke fama da matsalar daba. Sannan akasarin jihohin ƙasar na fama da yawaitar mutane da ke fama cikin ƙangin talauci A jihar Adamawa zaɓen ya ɗauki sabon salo, inda a karon farko cikin tarihi ake da ƴar takarar gwamna mace, a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar. Wannan wani muhimmin mataki ne a siyasar ƙasar, wadda mata ke a sahun baya wajen yin takara a muhimman muƙamai. Akwai yiwuwar wannan mataki zai ƙara wa mata azama wajen takarar manyan muƙamai a ƙasar Talla

Tsadar rayuwa ta ƙaru a Najeriya - NBS

Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta ce an samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairun 2023. Hukumar ta ce ta sanar a ranar Laraba cewa hauhawar farashin kayayyakin ya haura zuwa kashi 21.82 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 21.34 cikin dari a watan Disamba. Rahoton ya yi nuni da cewa hauhawar farashin kaya a shekara ya kai kashi 6.22 bisa ɗari idan aka kwatanta da na watan Janairun 2022, wanda ya kai kashi 15.60. Rahoton ya ce kayayyakin da farashinsu ya tashi sun haɗa da burodi wanda ya kai kashi 21.67 da dankali da dawa, da doya da kuma na kayan lambu. Bugu da ƙari, rahoton ya bayyana cewa farashin kayayyakni a cikin Janairu 2023 yana kashi 1.87 a kowane wata. Haka na zuwa ne yayin da 'yan ƙasar ke ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin sabbin takardun kuɗi sakamakon sake fasalin kuɗi da gwamnati ta yi. Matsalar ta jefa ‘yan ƙasar da dama cikin wahalhalu, inda suke fuskantar kalubale wajen biyan bukatun yau da kullum. Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta yi ga

Ana zargin malamin Islamiyya da yin lalata da yara huɗu a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce ta kama wani matashi mai shekara 38 malamin Islamiyya bisa zargin lalata da wasu yara mata guda huɗu duka ƴaƴan mutum ɗaya. Rundunar ta tabbatar da kama malamin kamar yadda mai magana da yawunta, DSP Mahid Mu’azu Abubakar ya yi wa BBC ƙarin bayani. A cewarsa yaran da abin ya rutsa da su ƴan shekara 12 ne da tara da kuma takwas. "Ba asalin malaminsu ba ne, yana zaune ne a makarantar Islamiyya ɗin, idan suka zo biya karatu, babban malami zai ce su je wajen wanda ake tuhuma da laifin domin su biya masa, sai yake amfani da wannan dama wajen yin lalata da yaran." in ji kakakin rundunar. Ya ce an ɗauki lokaci matashin yana cin zarafin ɗaliban kasancewar yaran ƙanana ne da ba sa iya yi wa iyayensu bayanin abin da ke faruwa da su a makaranta.