#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

Obasanjo ya bukaci kotun Birtaniya ta sassauta wa Ekweremadu hukunci

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya rubuta wa jami'an kotu a Birtaniya , inda yake bukatar a yi sassauci lokacin yanke wa sanatan Najeriya Ike Ekweremadu da matarsa hukunci bayan kama su da laifin 'safarar sassan jikin ɗan bil'adama.'

A watan da ya gabata ne kotu ta samu sanata Ike Ekweremadu mai shekara 60 da matarsa Beatrice da kuma wani likita Dr Obinna Obeta da laifin ɗaukar wani matashi ɗan shekara 21 daga Legas zuwa Birtaniya domin cire ƙodarsa, domin a bai wa ƴarsa Ekweremadu, mai suna Sonia, mai shekara 25.

A wasikar da Obasanjo ya rubuta, ya ce abin da ma'auratan suka yi ba daidai ba ne kuma babu wata al'umma da za ta lamunci aikata hakan.

Sai dai ya bukaci kotun da ta duba lamarin ƴar sanatan wadda lafiyarta ke cikin haɗari da kuma ke son agajin lafiya na gaggawa domin sassauta masa.

Obasanjo ya kuma faɗa wa kotun cewa ta duba ɗabi'u masu kyau da Ekweremadu ke da su a lokacin yanke masa hukunci.

Sai dai babu tabbacin cewa ko wasikar da Obasanjo ya rubuta za ta iya yin tasiri.

Tsohon shugaban ƙasar dai bai bayyana cewa ko yana magana da yawun gwamnatin Najeriya ba ne.

Sanata Ekweremadu da matarsa na tsare a hannun jami'an Birtaniya har zuwa 5 ga watan Mayu lokacin da za a yanke masa hukunci, karo na farko da ake yanke wa wani hukunci karkashin hana bauta ta zamani.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano