#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

‘Yan Arewa na shirin maye gurbin Tinubu da Shettima – Naja’atu Mohammed

Naja’atu Mohammed, ta bayyana shirin da ‘yan Arewa ke yi na maye gurbin dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da abokin takararsa, Kashim Shettima. Naja’atu ta yi ikirarin cewa wasu ’yan Arewa ne ke kira ga Tinubu ya ci gaba da cewa Shettima zai maye gurbinsa idan lafiyarsa ta tabarbare kuma ya gaza.

Da take magana da jaridar ThisDay, Naja’atu ta ce: “Suna so ne kawai su tura shi ya zama shugaban kasa. Ko da bai dace da sha’awarsa ba.”

“Wasu mutane daga Maiduguri sun kira ni yau suna tambayar, ‘Hajiya, me ya sa kika yi haka? Yanzu kina sukar kudirinmu. Danmu zai zama shugaban kasa, amma kina magana irin wannan? Bayan haka ma, yanzu dubi Tinubu; ba zai iya ba. Mu duka don Kashim muke yi. Ba ki kyautata mana ba.”

Naja’atu ta kuma yi ikirarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai damu da tattalin arziki, tsaro, ko kuma wanda zai gaje shi a matsayin shugaban kasa ba.

Ta bayyana cewa, duk da bayanan da aka samu daga dukkan hukumomin tsaro, shugaban bai damu da hadarin da Bola Tinubu ke ciki ba, idan aka yi la’akari da kalubalen da ake zargin sa na rashin lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano