#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

Zan yi nesa da Abuja idan na sauka daga mulki - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai koma mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, idan ya miƙa ragamar mulki ga sabuwar gwamnati mai zuwa a ranar 29 ga watan Mayu.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, ya ce Buhari ya faɗi haka ne jiya Laraba lokacin da ya karɓi bakuncin Jakadiyar Birtaniya a Najeriya mai barin gado, Catriona Wendy Laing.

Buhari ya yaba wa ƙasar Birtaniya kan tallafa wa Najeriya a ɓangarori da dama, musamman ma wajen sake gina yankin arewa maso gabas da ayyukan ƴan tayar da ƙayar-baya ya ɗaiɗaita.

Ya ce Birtaniya ta kasance gida ga ƴan Najeriya da dama, inda ya ce dangataƙar ƙasashen biyu za ta ci gaba da wanzuwa.

Tun da farko, Jakadiyar Birtaniyar ta ce ba ta jin daɗi barin Najeriya da za ta yi, musamman ma ganin cewa ta saba da abubuwa da dama a ƙasar, kamar al'adu da raye-raye da kuma wakokin ƴan ƙasar masu daɗi.

Ta ce ta ji daɗin kasancewarta a Najeriya, inda ta ce ta ziyarci jihohi sama da 20. Ta ce "na faɗa wa wanda zai gaje ni da shi ma idan ya zo ya rika yin irin abubuwan da na yi.

Ta kuma yaba wa shugaba Buhari kan samun nasarar kammala wa'adin mulkinsa na shekara takwas, inda ta ce ya yi kokari matuka wajen tafiya da ƴan ƙasar gaba-ɗaya.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano