#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

An ga watan Sallah a Najeriya

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce ganin jinjirin watan da aka yi a a kasar ya sanya ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1444.

Kwamitin tantance ganin wata karkashin jagorancin Maigirma Wazirin Sakkwato Farfesa. Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan a bana.

Cikin sanarwar da ya yi Sarkin Musulmi ya ce "mun samu bayanai daga wurare daban-daban a Najeriya kuma mun zauna da masana domin tabbatar da ingancin waɗannan bayanan gabanin mu sanar da al'umma cewa an ga watan.

Domin haka gobe Juma'a 21 ga watan Afrilu 2023 ita ce 1 ga watan Shawwal 1444," in ji Sarkin Musulmi.

Ya yi kira ga sauran musulmin ƙasar da su ajiye azumi domin an ga wata, su kuma yi shirin zuwa masallaci domin halartar Sallar Idi a wurare daban-daban.

Akasarin Musulmai a fadin duniya dai sun tashi da Azumin watan Ramadan ranar 23 ga watan Maris 2023.

Ya kuma yi addu'a kan Ubangiji ya karɓi ibadun da musulmi suka yi a faɗin duniya.

Sannan ya yi wa Najeriya addu'ar zaman lafiya da kuma rokon Allah Ya taimaki sabbin shugabannin da aka zaɓa a ƙasar kwanakin da suka gabata.

Saudiyya tuni ta sanar da ganin watan a garin garin Tumair wanda hakan ke nufin ranar Juma’a ne sallah. Ko da yake da farko sai da ta ba da sanarwar ba a ga watan ba a lardun gashin ƙasar.

A Iran kwamitin ganin watan ƙarƙashin jagorancin shugaban addini na ƙasar Ali Kamenei ya ce ba a ga watan ba, don haka sallah sai ranar Asabar.

Ku latsa nan don kallon bidiyon sanarwar daga bakin Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano