#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

Cire tallafin man fetur: Bankin Duniya ya baiwa FG $800m don bayar da tallafi

Babban Bankin Duniya ya ba wa gwamnatin Najeriya dala miliyan 800 domin ta samar da wani tsari mai inganci ga ‘yan kasarta, kafin a cire tallafin man fetur nan da watan Yunin 2023.

Ministan kudi, kasafin kudi da kuma Tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa (FEC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewar Ahmed, gwamnatin Najeriya ta kuduri aniyar kawo karshen tallafin man fetur nan da watan Yuni, don haka ta fara wani yunkuri na rage wa ‘yan kasar damuwa. Ta yi nuni da cewa, tuni aka samu kyakkyawar alaka da sabuwar majalisar rikon kwarya ta shugaban kasa (PTC) da kuma gwamnati mai zuwa, da nufin tafiyar da shirin.

"Mun samu makudan kudade da suka kai dala miliyan 800 daga bankin duniya domin tafiyar da ayyukan jin kai, kuma muna tunkarar gidaje kusan miliyan 10 ko kuma 'yan Najeriya miliyan 50 masu rauni a matakin farko." In ji Ministan yayin da take zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin jihar.

Ta lura cewa kaso mai yawa na kudaden zai kai ga gidaje miliyan 10 da ake ganin sun fi fama da rauni, don rage tasirin cire tallafin.

“A halin yanzu muna shigar da dukkan masu ruwa da tsaki. Mun san cewa ana yin la'akari da tsare-tsare daban-daban, gami da buƙatar motocin bas don ma'aikata, da wasu tsare-tsare da yawa na kwantar da hankali, ”in ji ta.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano