#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

Jerin Gwamnoni Takwas da suka yi tazarce

ranar Asabar 18 ga watan Fabrairu aka gudanar da zaɓen gwamnoni da kuma na ƴan majalisun dokoki na jihohi a Najeriya.

Yayin da aka sanar da sakamakon wasu jihohi, wasu kuma ana ci gaba da tattara sakamakon.

Ga jerin gwamnoni da suka yi tazarce a kan kujerunsu a zaɓen da aka gudanar.

Lagos

Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe na jihar Legs, Professor Adenike Temidayo Oladiji ya bayyana gwamna ma ci Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya samu nasarar komawa kan mulki karo na biyu. Sanwo Olu ya samu nasara ne da ƙuri'u 762,134.

Gombe

A jihar Gombe ma, hukumar zaɓe ta hannun jami'ar tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar, Farfesa Maimuna Waziri ta ayyana Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya yi nasarar sake ɗarewa kan mulki da kuri'u 345,821.

Kwara

Hukumar zaɓe a jihar Kwara, ta ayyana gwaman mai ci AbdulRahman AbdulRazaq a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamna. AbdulRahman ya koma kan mulki ne bayan samun nasara a illahirin kananan hukumomi 16 na faɗin jihar.

Yobe

A jihar Yobe ma, gwamna Mai Mala Buni ne ya samu nasarar komawa kan karagar mulki. Mai Mala Buni ya samu nasara ne da kuri'u 317,113, inda ya doke abokin karawarsa Sheriff Abdullahi na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 104,259.

Oyo

Gwamna Seyi Makinde na jam'iyyar PDP, shi ya lashe zaɓen gwamnan jihar. Makinde wanda shi ne gwamna mai ci ya samu ƙuri'u mafi yawa inda ya bai wa babban ɗan adawa a jihar, Teslim Folarin na Jam'iyyar APC tazarar ƙuri'u kusan dubu 300.

Ogun

A can jihar Ogun ma, gwamna Dapo Abiodun ne ya ci zaɓen gwamnan jihar da da aka yi a ranar Asabar. Ya samu nasara a karo na biyu ne bayan samun kuri'u 276,298, inda ya doke abokin hamayyarsa Ladi Adebutu na jam'iyyar PDP wanda ya samu ƙuri'u 262,383.

Nasarawa

A jihar Nasarawa ma, hukumar zaɓe ta sanar da gwamna mai ci Abdullahi Sule a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamnan jihar. Jami'in tattara sakamako zaɓen gwamnan jihar Ishaya Tanko, shi ya sanar da hakan a Lafiya babban birnin jihar. Abdullahi Sule ya samu damar komawa kan karagar mulki ne da kuri'u 347,209.

Bauchi

Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya sake ɗarewa kan mulki karo na biyu a sakamakon zaɓen gwamna da aka sanar a ranar Litinin. Jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya ce Bala Ƙaura ya samu nasara ne da ƙuri’u 525,280. Ya doke babban abokin hamayyarsa Air Marshal Abubakar Sadique Baba na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’u 432,272.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano