#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

Zakuna sun kashe shugabansu bayan sun yi masa tawaye

Dandazon ma’aikata da masu ziyarar yawon buɗe ido a wani lambun shakatawa na cigaba da bayyana alhininsu bisa tsautsayin da ya fada wa wani shahararren zaki Bob Junior, wanda aka fi sani da suna Snyggve a shafukan intanet.

Zakin mai saukin hali, wanda hotunansa ke ɗaukar hankali a shafukan sada zumunta, na da matukar kima a idon abokan hamayyarsa, ya kuma shugabancin namun dawan da ke dajin Serengeti na ƙasar Tanzaniya.

Inda ya shafe tsawon shekara bakwai yana zuba mulki a dajin tare da taimakon ɗan uwansa mai suna Tryggve.

Ana fargabar wasu ƙananan abokan hamayyarsa ne suka kashe shi.

Fredy Shirima, jami’i mai kula da gandun dajin na Serengeti, ya tabbatarwa da BBC faruwar lamarin.

Ya ce “yawancin irin wannan al’amari yana faruwa ne a lokacin da shugaban dawa da ke mulki ya tsufa, ko kuma a wasu lokuta, idan mazajen zakuna ba sa farin ciki da yadda ake tafiyar da gandun dajin," a cewar jami’in.

"Ana fargabar shima ɗan uwan nasa ya gamu da ajalinsa, sai dai muna ƙoƙarin tabbatar da hakan," inji Mr Shirima.

Ya ƙara da cewa, an kashe ‘yan uwan biyu ne a lokuta daban-daban amma dai harin da aka kai musu shiryayye ne.

Wasu masana gandun daji sun bayyana cewa Bob Junior - wanda ake kyautata zaton ya kai shekaru 10 da haihuwa - ya ɗare kan karagar mulkin gandun dajin ne bayan rasuwar mahaifinsa mai suna Bob Marley, wanda ya shahara saboda kyawun halayyarsa a lokacin da yake raye.

Rahotanni sun bayyana cewa sarkin zakin Bob Junior, ya mutu ne a sanadiyyar harin da aka ƙaddamar masa kuma aka yi galaba a kansa sannan aka kasheshi a ranar Asabar.

Jami’an dake kula da gandun dabbobi suna shirye-shiryen gudanar da jana’iza ta musamman a wata rana ta daban da ba a bayyana ba.

Dajin Serengeti da ke arewacin ƙasar Tanzania, ya kasance gidan zama ga zakuna kusan 3,000, kuma ya shahara matuƙa ga masu yawon buɗe-ido na cikin gida da ƙasashen waje.

Masu tafiyar da aikin yawon buɗe-ido a ƙasar na cigaba da wallafa sakonnin jinjina a shafukan intanet bisa rasuwa sarkin dajin.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano