#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

NDLEA ta kama basaraken gargajiya da laifin safarar ƙwaya

Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami'antsa sun kama wani Basaraken gargajiya da tubabben ɗan Boko Haram da wasu mutum 35 bisa laifin safarar muggan ƙwayoyi.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta Twitter mai ɗauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar Femi Babafemi, ta ce ta samu nasarar kama muggan ƙayoyin a cikin na'urar daskarar da abubuwa ta 'firinji' da kuma tukwanen gas a filin jirgin sama na Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Sanarwar ta ƙara da cewa jami'an hukumar sun kuma lalata gonakin da ake noma tabar wiwi da girmansu ya kai hekta 39.8 a jihohin Edo da Ondo.

Basaraken gargajiyar mai suna Baale Akinola Adebayo - sarkin Kajola, garin da ke kan iyakar jihohin Edo da Ondo - na daga cikin mutum 27 da hukumar ta ce ta kama da laifin safarar ƙwayoyin da nauyinsu ya kai tan 2.2 a faɗin jihohin ƙasar 12 cikin makon da ya gabata. Haka kuma hukumar ta ce ta kama Alayi Modu - wanda ya ƙwashe shekara 15 yana cikin ƙungiyar Boko Haram - kafin ya miƙa wuya a shekarar 2021.

Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai ritaya ya jinjina wa jami'an hukumar a jihohin ƙasar 12 bisa namijin ƙoƙarin da ya ce sun yi wajen kamen miyagun ƙwayoyin.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano