#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

Sarkin Kano Aminu Ado ya taya Abba Kabir murnar zama gwamna

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga watan Maris.

Cikin wata wasiƙa da ya aike da ita, Sarkin Kano ya ce ya fahimci mutane sun karɓi dimokradiyya hannu biyu-biyu, kuma abu mafi mahimmani shi ne yadda suka fito suka kaɗa kuri'unsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Gabanin haka shi ma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya aike da ta shi wasiƙar taya murna ga sabon zaɓaɓɓen gwamnan, wanda ya ce a madadinsa da iyalansa ya aika sakon.

Sarkin Rano ma Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa ya aike da na shi saƙon tare da fatan Allah ya taya sabon shugaban riƙo da shugabancin mutanen Kano.

Duka sarakunan sun miƙa godiya ga malaman addinai da shugabannin jama'a da suka riƙa wayar da kan al'umma, aka yi zaɓe lafiya aka gama lafiya.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano