#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

Canjin kuɗi : Har yanzu jama'a na shan baƙar wahala a Najeriya

Jama'a a Najeriya na ci gaba da fuskantar wahala ta samun takardun kudi a bankuna duk da alkawarin da babban bankin kasar ya yi cewa kudaden za su wadata daga ranar Alhamis 23 ga watan nan na Maris.

A ranar Laraba ne babban bankin, ya umurci bankuna da su je rassan CBN na jihohi su karbi tsofaffin takardun kudaden da suka ajiye don saukaka wa jama’a matsalar karancin kudin da ake fama da ita.

Ana ganin babban bankin ya bayar da wannan sanarwa ne bayan da kungiyar kwadago ta kasar NLC ta yi barazanar mamaye dukkanin ofisoshin bankin da ke jihohi ciki har da Abuja domin tilasta wa gwamnati ta dauki matakin na saukaka wa jama'a halin da ake ciki.

NLC ta ce daga mako mai zuwa ne za ta mamaye ofisoshin bankin domin hana su gudanar da ayyukansu.

To sai dai a binciken da BBC ta yi daga rahotannin da ta samu daga wakilanta a wasu sassan kasar har yanzu al'amarin ba sauki ta yadda jama'a ba sa samun isassun kudin walau sababbi ko ma tsofaffin a cikin bankunan da ma na'urar cirar kudi ta ATM.

Wakilinmu da ya kewaya sassan birnin Kano a wasu bankunan ya iske dogayen layuka na jama'a a na'urorin ATM da kuma cincirindon jama'a a haranar bankunan inda ya zanta da wasu da ya samu a wuraren.

Wani daga cikin mutanen da ya iske a layi ya ce masa, ''A halin da ake ciki gaskiya ni kam na zo banki kuma ban samu kudi ba.

''Amma dai an yi maganar an ce za a saki kudi amma ba a saki ba don kowa korafin da yake yi ke nan a cikin bankin, duka da ATM da ciki din duka ba kudin gaskiya.

''Kowa ma korafin da yake yi ke nan ba kudi suna bai wa mutane hakuri ne kawai,'' in ji shi.

Ita kuwa wata mata da BBC ta yi magana da ita a wani bankin ta ce da kyar ta samu naira dubu biyar, ga kuma tana tsananin bukatar kudin don zuwa asibiti, kamar yadda ta ce.

''Muna bukatar kusan naira dubu 200 ne amma suka ce sai dubu biyar kawai zan samu, ga azumi ga ba kudi ga ni ba ni da lafiya ma,'' in ji ta.

Bayan gani tare da tattaunawa da jama'a a wajen wasu bankunan wakilin na BBC ya samu shiga cikin wasu daga cikin bankunan inda ya iske jama'a dankam a ciki, wasu daga cikin mutanen suna zaune wasu kuwa suna kan layi.

Kuma bayanan da ya samu na cewa, bankin ba ya bayar da fiye da naira dubu goma saboda karancin kudaden.

Wani daga cikin mutanen ya yi masa bayani inda ya ce,'' yanzu matsalar kudin nan ka ga ni na kai wajen awa daya a na a zaune idan ba bankinka ba ne suna bada naira dubu daya sau daya idan ka yi na biyu za su ba ka dubu daya ka ga dubu biyu kenan.''

''Idan kuma birancinka ne za su ba ka naira dubu goma a wuni,'' in ji shi

BBC ta yi kokarin ji daga bakin jami’in hulda da jama’a na babban bankin Najeriyar CBN, Abdulmumini Isa don jin halin da ake ciki game da wannan matsala.

To amma bai amsa kiran waya ba kuma har zuwa lokacin hada wannan rahotan bai amsa sakon da aka aika masa ba.

Sai dai wani jami’i da ya bukaci da kada a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa zuwa ranar juma'a 24 ga watan nan na Maris ake fatan kudaden za su wadata bayan bankunan sun kammala wasu shirye-shriye.

Al'ummar Najeriya sun shiga wahala a sakamakon tsarin da gwamnatin kasar ta bullo da shi ta hanyar babban bankin inda ta sauya wasu daga cikin manyan takardun kudin kasar na naira 200 da 500 da kuma 1,000.

Abin da ya sa gwamnonin jihohi uku - Kaduna da Zamfara da Kogi suka kai kara kotun kolin kasar, kuma daga baya wasu jihohin suka mara musu baya

Kotun ta zartar da cewa matakin dakatar da amfani da tsofaffin kudin da gwamnati da babban bankin suka dauka ya saba doka saboda haka ta zartar da cewa a ci gaba da amfani da su har zuwa ranar 31 ga watan Disamba na wannan shekara ta 2023.

To amma daman kafin wannan hukunci sakamakon matsi da sukan gwamnati shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar da dama a ci gaba da amfani da tsohuwar takardar naira 200.

Matakin canjin kudin ya jefa al'ummar Najeriya musamman masu karamin karfi cikin matsi, abin da wasu ke ganin har ma ya durkusar da wasu kananan sana'o'i da kasuwanci.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano