Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya bayyana jagorancin Rasha a MDD da cewa tamkar wata mummunar tsokana ce.
Rasha dai ita ce ake sa ran zata karbi shugabancin karba-karba na MDD na kwanaki 30 a ranar Asabar.
Sai dai Mista Kuleba yace, Rasha ta jagoranci laifukan yaki, kuma ta shirya yaki na salon mulkin mallaka kan Ukraine.
Ya ce duniya zata yi bankwana da zaman lafiya, muddin Rasha ta samu bakin magana. Rasha dai na daga cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na MDD.
Comments
Post a Comment
Rubuta Sharhinku