#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

YANZU-YANZU: Ƴan daba sun tarwatsa masu zaɓe a wasu sassan Najeriya

Rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriya na cewa ƴan daba sun tarwatsa masu zaɓe a sassan ƙasar.

Kano:

Wani hoto ya nuna yadda masu matasa da ake zargin ƴan daba ne sun tarwatsa kayan zaɓe, suka kuma kori jama'a a ƙaramar hukumar Rogo. Lamarin ya faru ne a a lokacin da ake zaɓen gwamnnoni da na ƴan majalisun dokoki.

Lagos:

Rahotanni daga kafofin sada zumunta da dama sun nuna cewa an samu tashin hankali a wasu rumfunan zaɓe a cibiyar kasuwancin ƙasar ta Najeriya.

Wata tauraruwar fina-finan Nollywood Chioma Akpotha ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram inda ta yi zargin cewa wasu mutane sun kai mata hari da wuƙa.

"Ban iya ma fito da waya ta ba lokacin da yaran nan suka zo, suka ringa dukan motata, suka fasa min madubin gefe na mota..." tana magana ne a lokacin da take barin rumfar zaɓen.

Bayelsa:

Rahotanni na cewa wasu ƴan daba sun kwace tare da lalata kayan zaɓen ɗan majalisar dokoki a rumfuna masu lamba 02 da 03 da 04 da kuma rumfa ta 05 a mazaɓa ta biyar a ƙaramar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa, kamar yadda kafofin yaɗa labarai na jihar suka rawaita.

A nasa ɓangaren, gwamna Douye Diri ya yi Allah wadai da da harin da kakkausar murya, yana mai kira ga babban sufeton ƴan sanda na ƙasa da kwamishinan ƴan sandan jihar Bayelsa su maido da zaman lafiya a yankin, kamar yadda mai taimaka masa a harkokin kafofin watsa labarai Daniel Alabrah ya tabbatar a shafinsa na Faceook.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano