#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

Zargin kafa gwamnatin riƙo a Najeriya abin fargaba ne - Jam'iyyu

Kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyun Najeriya ya ce zargin kafa gwamntin riƙo a ƙasar, babban abin tayar da hankali ne da cusa fargaba.

Shugaban kwamitin, Engr Yabagi Sani ya ce “Ba ma mu ‘yan siyasa ba kaɗai ba, duk wanda ke kishin Najeriya, yake da kishin ci gaban Najeriya, yake kishin dimokraɗiyya ta kafu a Najeriya.

Idan aka dubi matsayin Najeriya ba ma a Afirka kaɗai ba, a duniya gaba ɗaya, abin da DSS ta fito da shi, abu ne na fargaba”.

Engr. Sani na mayar da martani ne kan zargin da DSS ta yi cewar wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a ƙasar na shirya maƙarƙashiyar kafa gwamnatin riƙon ƙwarya don hana rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasa nan gaba cikin wata Mayu.

Ya ce a ganinsa, abin da ya janyo kitsa irin wannan maƙarƙashiya da ake zargi, shi ne rashin gamsuwar da mai yiwuwa wasu ‘yan siyasa ke da ita kan zaɓukan 2023 da kammala a baya-bayan nan.

"Lallai waɗanda ba su gamsu da abin da hukumar zaɓe ta fito da shi ba ne, mai yiwuwa cikinsu ne aka samu waɗanda ke nuna fushinsu," in ji Engr Sani.

Engr Yabagi Sani ya ce alhakin hukumar DSS ne ta ɗauki mataki, kuma ta fito ta yi wa jama’a bayani game da binciken da suka gudanar da kuma abin da suka gano saboda sun san girman illar da irin wannan maƙarƙashiya za ta iya haddasa wa dimokraɗiyyar Najeriya.

A cewarsa, irin wannan zargi idan aka samu waɗanda ke yunƙuri ko kuma suna cikin aikatawa, to ya kamata a ɗauki mataki, ba wai a fito a bayyana wa jama’a ba.

“Idan an gaya wa jama’a, to me za su yi?” Yabagi ya tambaya.

Ya ce tun da DSS ta yi iƙirarin cewa ta san ‘yan siyasar da ke kitsa wannan maƙarƙashiya, to kamata ya yi idan lokaci da halin a faɗa wa jama’ar ya yi, sai ta fito ta bayyana sunayen mutane da ke shiryawa da kuma matakin da ta ɗauka a kan su.

“To ta nan ne jama’a za su yarda, amma yanzun in ba a yi hankali ba, za a ma ce su DSS ɗin nan me suke nufi da irin wannan magana da suka yi?”

Da aka tambaye shi ko yana da masaniya a kan wannan shiri na kafa gwamnatin riƙo da DSS ta yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa irinsa na kitsawa, sai shugaban kwamitin gamayyar jam’iyyun Najeriyar ya ce “A’a, wannan ai kamar ana so a shafa wa ‘yan siyasa kashin kaji ne kawai.

Idan gaskiya ne a fito a gaya mana cewa su wane kaza ne, kuma ga abin da suka yi. Shi ya sa na ce, mu ba mu yarda da wannan ba. Su fito su gaya wa jama’a ƙarara cewa ga abin da yake faruwa”.

Wanne zargi DSS ta yi?

A ranar Laraba ne hukumar jami'an tsaron farin kaya ta Najeriya ta tabbatar da raɗe-raɗin cewa akwai wata ƙullaliya da wasu 'yan siyasa ke kitsawa don ganin an kafa gwamnatin riƙo a ƙasar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta DSS, Peter Afunanya ya sanya wa hannu ta ce “wani yunƙuri ne na jingine tsarin mulki da yin zagon ƙasa ga mulkin farar hula da kuma yunƙurin jefa ƙasar cikin ruɗani.”

Sanarwar ta ƙara da cewa “masu kitsa lamarin sun tattauna kan hanyoyi da dama na aiwatar da shirin nasu, kamar haddasa mummunar zanga-zanga a manyan biranen Najeriya, wadda za ta haifar da ƙaƙaba dokar-ta-ɓaci.”

“Ko kuma ta hanyar nemo izinin kotu domin dakatar da rantsar da sabuwar gwamnati da majalisar dokokin tarayya, ta hanyar da ba ta dace ba.”

Ma'anar gwamnatin riƙon-ƙwarya

Gwamnatin riƙon-ƙwarya na nufin gwamnatin wucin-gadi ko kuma gwamnatin da ake kafawa na wani ɗan lokaci.

Wasu kuma kan kira ta gwamnatin miƙa mulki.

Ana kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya ne domin ta yi aiki kafin samar da zaɓaɓɓiyar gwamnati mai zuwa.

A mafi yawan lokuta babban aikinta shi ne tsara harkokin siyasa da kuma yadda za a yi zaɓe domin samar da sabuwar gwamnati.

Manyan masu riƙe da lamurran ƙasa ne ke zaɓen waɗanda za su jagoranci irin wannan gwamnati, mafi yawan lokuta a lokacin da aka kawo ƙarshen wani yaƙin basasa.

Haka kuma, ana kafa irin wannan gwamnati a duk lokacin da aka soke zaɓe a ƙasa mai bin tafarkin dimokraɗiyya, bayan cikar wa’adin gwamnati mai ci.

A Najeriya an kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙarshe ne shekaru 30 da suka gabata, a 1993, lokacin da gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta soke zaɓen da aka gudanar, wanda ake yiwa laƙabi da June 12.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano