#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

Ƙungiyar ƴan a-waren Biafra, IPOB ce ta goma a duniya a ta'addanci - Rahoto

Haramtacciyar ƙungiyar ƴan a-ware ta Biafra, (IPOB) da ke kudancin Najeriya ta zama ta goma a cikin ƙungiyoyin da suka fi aikata ta'addanci a duniya.

Wata ƙididdiga da rahoto (Global Terrorism Index (GTI) na wannan shekara ta 2023 da aka fitar na duniya game da ta'addanci wanda ya sanya ƙungiyar a wannan mataki, ya ce hare-hare 40 da kisan gilla 57 da ta aikata a 2022 su suka sa ta kai wannan mataki.

Daga cikin kisan gillar da IPOB din ta aikata akwai na hallaka wasu sojojin Najeriya ango da amarya, wadanda ta gille musu kai, da kisan 'yan arewacin kasar da ke kudu maso gabashi da kuma kisan jami'an tsaro da dama.

Rahoton wanda ya bayyana ƙungiyar ta IPOB da cewa mai haɗarin gaske ce a ta'addanci, ya sanya Al-Shabaab a matsayin ta ɗaya a duniya wajen ta'addanci.

Ƙungiyar ta Al-Shabaab wadda take da ƙarfi a gabashin Afirka rahoton ya nuna cewa ta yi kisan gilla 784 da hare-hare 315, yayin da ƙungiyar IS ta lardin Khorasan (ISK) ta yi kisa 498 da kuma hare-hare 141.

Sai kuma ƙungiyar Jamaat Nusrat Al-Islam wal Muslimeen (JNIM), wadda ta hallaka rayuka 279 da kai hari 77, yayin da Balochistan Liberation Army (BLA), ta hallaka rai 233 ta kai hari 30.

Ita kuwa ƙungiyar IS ta yammacin Afirka (ISWAP), ta kasance ta 6 a rahoton inda ta hallaka rai 219 da kai hari 65, yayin da Boko Haram ke bi mata baya da kisan kai 204 da hare-hare 64.

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano