#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

DA DUMU-DUMI: 'Yan sanda sun kubutar da ma'aikatan INEC 17, a jahar Imo

Jami’an ‘yan sanda a jihar Imo sun ceto ma’aikatan wucin-gadi na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) guda goma sha bakwai a jihar Imo.

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi garkuwa da jami’an hukumar ta INEC da aka tura zuwa mazabu goma 19 a karamar hukumar Ideato ta Kudu, a kan hanyarsu ta zuwa wajen da za su yi aiki daban-daban.

Sai dai an rawaito cewa ‘yan sandan sun yi gaggawar ceto su daga baya.

Da yake magana da manema labarai a ranar Asabar, mai magana da yawun hukumar ta INEC na jihar, Dr. Chineye Chijioke-Osuji, ya tabbatar da ceto jami’an.

Chijioke-Osuji, ya ce an ceto jami’an zaben ne ba tare da kayayyakin zabe ba da kuma na'urar (BVAS).

Talla