#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Juma'a 23, Yuni, 2023

INEC ta sanar da ranar sake zabe a Kebbi da Adamawa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta bayyana ranar da za a sake gudanar da zabukan jihohin Kebbi da Adamawa.

Babban Sakataren Yada Labarai na INEC, Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi ne, ya bayyana hakan a birnin Abuja.

Ya ce za a gudanar da zabukan gwamnoni da na wasu ‘yan majalisar tarayya da na jihohi a rana guda.

Yayin taron da ta gudanar a ranar Litinin, INEC ta yanke shawarar cewa za a gudanar da dukkanin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi a ranar Asabar, 15 ga Afrilu, 2023,” in ji Oyekanmi.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da cikakken bayani kan yadda zaben zai gudana a hukumance.

Rahotanni sun nuna cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi na ranar 18 ga watan Maris, an soke zabukan wasu mazabun, abin da ya sanya INEC ayyana sakamakon wasu jihohin a matsayin wadanda ba su kammala ba

Comments

Popular posts from this blog

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano