#Attribution1 {display; none;} Skip to main content

Posts

Showing posts from March, 2023

Juma'a 23, Yuni, 2023

Saudiyya ta ƙwace tan biyar na naman kaji da ya lalace

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Saudiyya (SFDA) ta ƙwace tan biyar na naman kajin da ya lallace a wani gidan ajiye kayyakin abinci da ke birnin Riyadh. Hukumar ta tabbatar da cewa gidan ajiyar kayan abincin ya saɓa wa ƙa'idoji masu yaw, cikin har da yin ƙarya sayar da kayayyakin da suka lalace, inda ake sake wa naman kajin mazubi tare da sanya musu sabbin kwanan watan lalacewa. Haka kuma hukumar ta ce gidan ajiyar ya saɓa wa dokokin lafiya, da amfani da ma'aikatan da ba su da takardun shaidar karatun lafiya. SFDA ta kuma rufe gidan ajiyar tare da lalata duk kayyakin da ta ƙwace. Hukumar ta ce ta gudanar da wannan aiki ne tare da hadin gwiwwar hukumar gudanarwar birnin Riyadh da ma'aikatar kasuwanci da ma'aikatar walwala da ci gaba jama'a da hukumar zakka da haraji ta ƙasar tare kuma da hukumar fasa ƙwauri ta ƙasar. Haka kuma hukumar ta yi kira ga kwastomomi da su kai rahoton duk wani shago ko kamfanin da ya sayar musu da kayayyakin da suka lal

Amurka ta ƙwace $53m daga hannun Diezani bayan kama ta da laifi

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta cimma matsaya kan wasu shari'u biyu da suka buƙaci ƙwace wasu manyan kadarori na alfarma da aka samar da su a ƙasar ta hanyar laifukan almundahanar kuɗaɗe. Wasu takardu daga ma'aikatar shari'ar ƙasar sun nuna cewa batun ya shafi tsohuwar ministar albarkatun man fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke da wasu abokan kasuwancinta biyu Kolawole Akanni Aluko da Olajide Omokore. Da wannan mataki a yanzu ma'aikatar shari'ar ƙasar ta ce ta ƙwace kuɗin da ya kai dala miliyan 53.1, ƙimar kuɗin kadarorin idan aka sayar da su. Takardun kotun sun nuna cewa daga shekarar 2011 zuwa 2015 Diezani wadda a lokacin take ministar man fetur a Najeriya ta karɓi cin hanci daga abokan kasuwancinta. Wadda ita kuma Diezani ta riƙa bai wa kamfanoninsu manyan kwangilolin man fetur. Ma'aikatar shari'ar Amurkan ta ce an yi amfani da kuɗaden da aka biya a matsayin cin hancin da yawansu ya kai sama da dala miliyan 100, wajen sayan manyan kada

Zargin kafa gwamnatin riƙo a Najeriya abin fargaba ne - Jam'iyyu

Kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyun Najeriya ya ce zargin kafa gwamntin riƙo a ƙasar, babban abin tayar da hankali ne da cusa fargaba. Shugaban kwamitin, Engr Yabagi Sani ya ce “Ba ma mu ‘yan siyasa ba kaɗai ba, duk wanda ke kishin Najeriya, yake da kishin ci gaban Najeriya, yake kishin dimokraɗiyya ta kafu a Najeriya. Idan aka dubi matsayin Najeriya ba ma a Afirka kaɗai ba, a duniya gaba ɗaya, abin da DSS ta fito da shi, abu ne na fargaba”. Engr. Sani na mayar da martani ne kan zargin da DSS ta yi cewar wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a ƙasar na shirya maƙarƙashiyar kafa gwamnatin riƙon ƙwarya don hana rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban ƙasa nan gaba cikin wata Mayu. Ya ce a ganinsa, abin da ya janyo kitsa irin wannan maƙarƙashiya da ake zargi, shi ne rashin gamsuwar da mai yiwuwa wasu ‘yan siyasa ke da ita kan zaɓukan 2023 da kammala a baya-bayan nan. "Lallai waɗanda ba su gamsu da abin da hukumar zaɓe ta fito da shi ba ne, mai yiwuwa cikinsu ne aka samu waɗan

Gobara ta tashi a kasuwar kayayyakin gyaran mota da ke jihar Legas

Getty ImagesCopyright: Getty Images Wata gobara ta tashi a kasuwar kayayyakin gyaran mota da na laturoni ta Olowu da ke jihar Legas. Gobarar ta tashi a kasuwar ne a daren da ya gabata, sai dai gobarar ta yi ɓarna kafin jami'an kashe gobara su kai ɗauki. Sai dai ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma wasu mutane na danganta tashinta ne da barin wutar lantarki a kunne yayin da dama kuma ke cewa tana da nasaba da siyasa. Wannan dai ita ce gobara ta uku cikin makwanni uku da aka samu tashinta a birnin Legas.

Ƴar fafutukar Saudiyya Salma al-Shebab ta shiga yajin cin abinci

Yar fafutukar nan ta kasar Saudiyya Salma al-Shehab, wadda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru 27 sakamakon bayanan da ta yaɗa a shafin Twitter, ta shiga yajin cin abinci. Kungiyar kare hakkin ɗan adam ta ALQST ta ce Mis al-Shehab da wasu mata bakwai da aka tsare a Saudiyyar, sun fara yajin cin abinci mako guda da ya gabata. Salma al-Shehab wadda ke karatun digirin digir-gir a ƙasar Birtaniya, an kamata ne a lokacin da ta koma gida hutu shekaru biyu da suka gabata. Ana tuhumarta ne da laifin taimaka wa masu sukar manufofin gwamnatin Saudiyya da ke neman tayar da zaune tsaye ta hanyar wallafa bayanai babu kakkautawa a shafin twita. Tun da farko dai an yanke mata hukuncin ɗaurin shekara shida, inda daga bisani aka mayar da shi shekaru 34, sannan aka rage zuwa shekaru 27.

Ukraine ta ce: "Duniya za ta yi bankwana da zaman lafiya da Rasha ta samu jagorancin MDD"

Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, ya bayyana jagorancin Rasha a MDD da cewa tamkar wata mummunar tsokana ce. Rasha dai ita ce ake sa ran zata karbi shugabancin karba-karba na MDD na kwanaki 30 a ranar Asabar. Sai dai Mista Kuleba yace, Rasha ta jagoranci laifukan yaki, kuma ta shirya yaki na salon mulkin mallaka kan Ukraine. Ya ce duniya zata yi bankwana da zaman lafiya, muddin Rasha ta samu bakin magana. Rasha dai na daga cikin kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na MDD.

Martanin jam'iyyu kan kammala zabuka

A Najeriya, tuni wasu `yan takara da ke dakon a kammala zabensu suka yi maraba da sanarwar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasar INEC, wadda ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu mai zuwa don kammala zaben gwamnoni da na`yan majalisun dokoki a wasu sassan kasar. Sanarwa INEC din ta kawo karshen dogon zaman jiran da al`umomin yankunan da zaben ya shafa da kuma `yan takara ke yi. Jihar Adamawa da Kebbi su ne jihohi biyu rak da ba a kammala zaben gwamna ba a Najeriyar. Tsohon ministan lafiya da harkokin wajen Najeriya kuma jigo a kwamitin yakin neman zaben gwamna Fintiri na jam’iyyar PDP a Adamawa, Dr Idi Hong, ya shaida wa BBC cewa, tsayar da ranar sake zaben za ta ba su damar sake shiri har su sake zuwa wuraren da aka soke zabensu don sake yada manufofinsu. Ya ce, “ Dama mu jam’iyyar PDP masu bin doka ne don haka za mu jira ranar da aka tsayar don sake zaben nan, idan aka yi zaben nan za a gane bambanci.” A jihar Kebbi ma zaben gwamnan da aka yi a zagayen farko, kamar yadda hukumar za

INEC ta sanar da ranar sake zabe a Kebbi da Adamawa

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta bayyana ranar da za a sake gudanar da zabukan jihohin Kebbi da Adamawa. Babban Sakataren Yada Labarai na INEC, Mista Rotimi Lawrence Oyekanmi ne, ya bayyana hakan a birnin Abuja. Ya ce za a gudanar da zabukan gwamnoni da na wasu ‘yan majalisar tarayya da na jihohi a rana guda. Yayin taron da ta gudanar a ranar Litinin, INEC ta yanke shawarar cewa za a gudanar da dukkanin zabukan gwamnoni da na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi a ranar Asabar, 15 ga Afrilu, 2023,” in ji Oyekanmi. Ya ce nan ba da jimawa ba za a fitar da cikakken bayani kan yadda zaben zai gudana a hukumance. Rahotanni sun nuna cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu da kuma zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi na ranar 18 ga watan Maris, an soke zabukan wasu mazabun, abin da ya sanya INEC ayyana sakamakon wasu jihohin a matsayin wadanda ba su kammala ba

PDP ta maye gurbin Iyioricha Ayu bayan dakatar da shi

Iyioricha Ayu lokacin da ya lashe zaben shugabancin jam'iyyar ta PDP. Iyioricha Ayu lokacin da ya lashe zaben shugabancin jam'iyyar ta PDP. Kwamitin ayyuka nababbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ya maye gurbin shugaban jam’iyyar Sanata Iyioricha Ayu. A wani taron gaggawa da jam’iyyar ta yi a ranar Talata, kwamitin ya amince da umarnin babbar kotun jihar Benue, wadda ta haramta wa Ayu bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar. Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce bayan yin nazari da kyau da umarnin kotu da kuma bin sashe na 45 (2) na kundin tsarin mulkin PDP da aka yi wa gyara a 2017, kwamitin ya yanke shawarar cewa Mataimakin Shugaban shiyyar Arewa, Ambasada Umar Ilyya Damagum shine zai rike shugabancin jam’iyyar. Rikicin jam’iyyar bayan zaben kasar, ya dauki wani sabon salo a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da masu ruwa da tsaki na gundumar Igyorov a karamar huk

Yadda za ku guje wa galabaita saboda tsananin zafi a lokacin azumi

Hukumar lura da yanayi ta Najeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa za a fuskanci tsananin zafi a wasu jihohin Najeriya. A wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi, NiMet ta ce yanayin wanda ake sa ran ya fara daga Litinin zai iya haura digiri 40 a ma'aunin salshiyas. Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da Kwara. Sai kuma birnin Tarayya Abuja da Nasarawa da Benue da Bauchi da Gombe da kuma Borno. Nimet ta ce za a fuskanci yanayin na zafin rana ne a tsawon kwanaki biyu masu zuwa. Nimet ta ce jihohin da makin zai haura 40 sun haɗa da wasu sassan Sokoto da Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa. Hukumar ta sharwarci mutane da ke zaune a jihohin da abin zai shafa, da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin. Sai dai lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da al'umma musulmi ke gudanar da azumin Ramadana a Najeriyar da ma sauran ƙasashen duniya.

Jadawalin Lokutan Sahur Da Buda Baki A Birnin Kano

Canjin kuɗi : Har yanzu jama'a na shan baƙar wahala a Najeriya

Jama'a a Najeriya na ci gaba da fuskantar wahala ta samun takardun kudi a bankuna duk da alkawarin da babban bankin kasar ya yi cewa kudaden za su wadata daga ranar Alhamis 23 ga watan nan na Maris. A ranar Laraba ne babban bankin, ya umurci bankuna da su je rassan CBN na jihohi su karbi tsofaffin takardun kudaden da suka ajiye don saukaka wa jama’a matsalar karancin kudin da ake fama da ita. Ana ganin babban bankin ya bayar da wannan sanarwa ne bayan da kungiyar kwadago ta kasar NLC ta yi barazanar mamaye dukkanin ofisoshin bankin da ke jihohi ciki har da Abuja domin tilasta wa gwamnati ta dauki matakin na saukaka wa jama'a halin da ake ciki. NLC ta ce daga mako mai zuwa ne za ta mamaye ofisoshin bankin domin hana su gudanar da ayyukansu. To sai dai a binciken da BBC ta yi daga rahotannin da ta samu daga wakilanta a wasu sassan kasar har yanzu al'amarin ba sauki ta yadda jama'a ba sa samun isassun kudin walau sababbi ko ma tsofaffin a cikin bankunan da ma

Sarkin Kano Aminu Ado ya taya Abba Kabir murnar zama gwamna

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga watan Maris. Cikin wata wasiƙa da ya aike da ita, Sarkin Kano ya ce ya fahimci mutane sun karɓi dimokradiyya hannu biyu-biyu, kuma abu mafi mahimmani shi ne yadda suka fito suka kaɗa kuri'unsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Gabanin haka shi ma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya aike da ta shi wasiƙar taya murna ga sabon zaɓaɓɓen gwamnan, wanda ya ce a madadinsa da iyalansa ya aika sakon. Sarkin Rano ma Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa ya aike da na shi saƙon tare da fatan Allah ya taya sabon shugaban riƙo da shugabancin mutanen Kano. Duka sarakunan sun miƙa godiya ga malaman addinai da shugabannin jama'a da suka riƙa wayar da kan al'umma, aka yi zaɓe lafiya aka gama lafiya.

Kotu ta samu Ekweremadu da laifin yunƙurin safarar sassan ɗan adam

Wata kotu a Birtaniya ta samu ɗan majalisar dattijan Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa da laifin yunkurin safarar sassan ɗan adam. Shari'ar ta shafi dauko wani dan Najeriya mai shekaru 21 zuwa Birtaniya domin a cire ƙodarsa a bai wa diyar Ekweremadun. Kotun ta kuma sami wani likita mai shekaru 50, Dr Obinna Obeta da haɗa baki da dan siyasar wajen samo mutumin saboda a cire masa koda. Masu shigar da kara sun ce za a cire kodar mutumin ne domin a saka wa Sonia, ɗiyar Ekweremadu mai shekaru 25. Kotun ta wanke Sonia da hannu a tuhumar da ake yi mata. Matashin da aka so amfani da ƙodar tasa, wani mai ƙaramar sana’a ne a birnin Legas. An kai shi Birtaniya ne a bara domin gudanar da aiki a asibitin Royal Free Hospital da ke biornin London. Ya ce an yi alƙawarin samar masa aiki a Birtaniya saboda taimakon da zai yi, sai dai ya ce ya gane cewa ana masa shigo-shigo ba zurfi ne bayan tattaunawa da likitoci a ƙasar ta Birtaniya. Duk da cewa ba laifi ba ne bayar da g

DA DUMI-DUMI: An ga watan azumin Ramadan a Najeriya

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na uku ya sanar da ganin jaririn watan Ramadan na shekarar 2023 a wasu sassan Najeriya. A jawabin da ya yi na sanarwar wanda aka sanya a shafin Tuwita na kwamitin ganin watan, Sarkin Musulmin ya ce an ga watan ne bayan samun rahotanni daga shugabannin addinin Musulunci da ke wasu jihohin ƙasar. Hakan na nufin ranar Alhamis 23 ga watan Maris din 2023 ne za ta kasance daya ga watan Ramadan.

Gwamnoni huɗu da zaɓe bai musu daɗi ba

An kammala zabukan shugaban ƙasa da na gwamnoni da kuma ƴan majalisar Dokoki na tarraya da kuma jihohi a fadin Najeriya. Zaben ya bar wadansu ƴan siyasa cike da murna yayin da wadansu ƴan siyasar suke cike da bakin ciki, saboda yadda sakamakon ya kasance. A waɗansu jihohin ƙasar an samu sauyi a jam’iyyar da ke mulki inda ƴan adawa suka samu nasara a yayin da a waɗansu kuma masu mulkin ne suka samu dama domin ci gaba da jan ragama. Bari mu duba jihohi huɗu da suka fi jan hankali, watau Kano da Zamfara da Sokoto da kuma Plateau. ‘Makomar Ganduje a Kano’ Tun bayan zaben shugaban ƙasa a jihar Kano inda jam’iyyar APC mai mulki ta sha kaye a hannun jam’iyyar adawa ta NNPP, alamu suka nuna cewa gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje sai ya dage idan har yana son ɗan takarar APC, Nasiru Gawuna ya ci zabe. Amma bayan kammala zaɓen gwamna a ƙarshen mako, sai jam’iyyar NNPP ta kwace ragamar jihar inda hukumar zabe ta ƙasa INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben gwam

Jerin Gwamnoni Takwas da suka yi tazarce

ranar Asabar 18 ga watan Fabrairu aka gudanar da zaɓen gwamnoni da kuma na ƴan majalisun dokoki na jihohi a Najeriya. Yayin da aka sanar da sakamakon wasu jihohi, wasu kuma ana ci gaba da tattara sakamakon. Ga jerin gwamnoni da suka yi tazarce a kan kujerunsu a zaɓen da aka gudanar. Lagos Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe na jihar Legs, Professor Adenike Temidayo Oladiji ya bayyana gwamna ma ci Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya samu nasarar komawa kan mulki karo na biyu. Sanwo Olu ya samu nasara ne da ƙuri'u 762,134. Gombe A jihar Gombe ma, hukumar zaɓe ta hannun jami'ar tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar, Farfesa Maimuna Waziri ta ayyana Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya yi nasarar sake ɗarewa kan mulki da kuri'u 345,821. Kwara Hukumar zaɓe a jihar Kwara, ta ayyana gwaman mai ci AbdulRahman AbdulRazaq a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamna. AbdulRahman ya koma kan mulki ne bayan samun nasara a illahirin kananan hukumomi 16 na faɗin jih

YANZU-YANZU: Ƴan daba sun tarwatsa masu zaɓe a wasu sassan Najeriya

Rahotanni daga sassa daban-daban na Najeriya na cewa ƴan daba sun tarwatsa masu zaɓe a sassan ƙasar. Kano: Wani hoto ya nuna yadda masu matasa da ake zargin ƴan daba ne sun tarwatsa kayan zaɓe, suka kuma kori jama'a a ƙaramar hukumar Rogo. Lamarin ya faru ne a a lokacin da ake zaɓen gwamnnoni da na ƴan majalisun dokoki. Lagos: Rahotanni daga kafofin sada zumunta da dama sun nuna cewa an samu tashin hankali a wasu rumfunan zaɓe a cibiyar kasuwancin ƙasar ta Najeriya. Wata tauraruwar fina-finan Nollywood Chioma Akpotha ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Instagram inda ta yi zargin cewa wasu mutane sun kai mata hari da wuƙa. "Ban iya ma fito da waya ta ba lokacin da yaran nan suka zo, suka ringa dukan motata, suka fasa min madubin gefe na mota..." tana magana ne a lokacin da take barin rumfar zaɓen. Bayelsa: Rahotanni na cewa wasu ƴan daba sun kwace tare da lalata kayan zaɓen ɗan majalisar dokoki a rumfuna masu lamba 02 da 03 da 04 da kuma rumfa ta 05 a mazaɓa ta

YANZU-YANZU: An dakatar da kada kuri'a a rumfunan zabe tara a jihar Taraba

An an dakatar da kada kuri’a a rumfuna tara a mazabun Gyetta Aure da Asibiti na karamar hukumar Donga a jihar Taraba. Zanga-zanga ta barke a wasu sassan jihar yayin da masu kada kuri'a a yankin suka yi zargin cewa kuri'un na bogi ne da takardar sakamakon zabe. ICRI ta bayyana cewa masu kada kuri’a a unguwannin Gyetta Aure da Asibiti na karamar hukumar Donga a yankin Taraba ta Kudu na zanga-zangar nuna rashin amincewa da gano takardun zabe na bogi da kuma takardar sakamakon zabe. Rahotanni sun ce zanga-zangar ta dakatar da kada kuri'a a rumfunan zabe tara na gundumar. Da yake bayar da bayanin yadda lamarin ya faru, wani mai lura da zaben ya ce a yanzu masu kada kuri’a sun karaya wajen kada kuri’a kan gano takardun zabe da sakamakon bogi da ake zargi. An kuma bayyana cewa, a lokacin da ake gabatar da rahoton, an mayar da dukkan kayayyakin zaben zuwa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke unguwar.

DA DUMU-DUMI: 'Yan sanda sun kubutar da ma'aikatan INEC 17, a jahar Imo

Jami’an ‘yan sanda a jihar Imo sun ceto ma’aikatan wucin-gadi na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) guda goma sha bakwai a jihar Imo. Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi garkuwa da jami’an hukumar ta INEC da aka tura zuwa mazabu goma 19 a karamar hukumar Ideato ta Kudu, a kan hanyarsu ta zuwa wajen da za su yi aiki daban-daban. Sai dai an rawaito cewa ‘yan sandan sun yi gaggawar ceto su daga baya. Da yake magana da manema labarai a ranar Asabar, mai magana da yawun hukumar ta INEC na jihar, Dr. Chineye Chijioke-Osuji, ya tabbatar da ceto jami’an. Chijioke-Osuji, ya ce an ceto jami’an zaben ne ba tare da kayayyakin zabe ba da kuma na'urar (BVAS). Talla <img alt="" border="0" height="320" data-original-height="1080" data-original-width="720" src="https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEivgSeNsTUTVtamKB34OxjFNjFbQ62jitxQ9Qa6goEmd1V_iGeOJX1ECI04mlV67Pry7i5nP9DEcd35DIn

Zaben Gwamnoni- Mene ne mutane za su yi la’akari da su?

Abubuwan da mutane za su yi la’akari da su wajen zaɓen gwamnoni sun banbanta daga wata jiha zuwa wata. Misali, matsalar cunkoson ababen hawa da ta muhalli da hanyoyin sufuri su ne manyan matsalolin da ke addabar jihar Legas. Jihohi irin su Kaduna, da Katsina da Zamfara kuwa na fama da matsalar tsaro. Akwai kuma jihohi irin Kano da Sokoto, da Bauchi waɗanda ke fama da matsalar daba. Sannan akasarin jihohin ƙasar na fama da yawaitar mutane da ke fama cikin ƙangin talauci A jihar Adamawa zaɓen ya ɗauki sabon salo, inda a karon farko cikin tarihi ake da ƴar takarar gwamna mace, a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar. Wannan wani muhimmin mataki ne a siyasar ƙasar, wadda mata ke a sahun baya wajen yin takara a muhimman muƙamai. Akwai yiwuwar wannan mataki zai ƙara wa mata azama wajen takarar manyan muƙamai a ƙasar Talla

Tsadar rayuwa ta ƙaru a Najeriya - NBS

Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta ce an samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairun 2023. Hukumar ta ce ta sanar a ranar Laraba cewa hauhawar farashin kayayyakin ya haura zuwa kashi 21.82 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 21.34 cikin dari a watan Disamba. Rahoton ya yi nuni da cewa hauhawar farashin kaya a shekara ya kai kashi 6.22 bisa ɗari idan aka kwatanta da na watan Janairun 2022, wanda ya kai kashi 15.60. Rahoton ya ce kayayyakin da farashinsu ya tashi sun haɗa da burodi wanda ya kai kashi 21.67 da dankali da dawa, da doya da kuma na kayan lambu. Bugu da ƙari, rahoton ya bayyana cewa farashin kayayyakni a cikin Janairu 2023 yana kashi 1.87 a kowane wata. Haka na zuwa ne yayin da 'yan ƙasar ke ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin sabbin takardun kuɗi sakamakon sake fasalin kuɗi da gwamnati ta yi. Matsalar ta jefa ‘yan ƙasar da dama cikin wahalhalu, inda suke fuskantar kalubale wajen biyan bukatun yau da kullum. Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta yi ga

Ana zargin malamin Islamiyya da yin lalata da yara huɗu a Gombe

Rundunar ƴan sandan jihar Gombe ta ce ta kama wani matashi mai shekara 38 malamin Islamiyya bisa zargin lalata da wasu yara mata guda huɗu duka ƴaƴan mutum ɗaya. Rundunar ta tabbatar da kama malamin kamar yadda mai magana da yawunta, DSP Mahid Mu’azu Abubakar ya yi wa BBC ƙarin bayani. A cewarsa yaran da abin ya rutsa da su ƴan shekara 12 ne da tara da kuma takwas. "Ba asalin malaminsu ba ne, yana zaune ne a makarantar Islamiyya ɗin, idan suka zo biya karatu, babban malami zai ce su je wajen wanda ake tuhuma da laifin domin su biya masa, sai yake amfani da wannan dama wajen yin lalata da yaran." in ji kakakin rundunar. Ya ce an ɗauki lokaci matashin yana cin zarafin ɗaliban kasancewar yaran ƙanana ne da ba sa iya yi wa iyayensu bayanin abin da ke faruwa da su a makaranta.

Hukumar NBC ta hukunta kafafen yaɗa labarai 25 saboda saɓa dokoki lokacin zaɓe

Hukumar kula da kafafen yaɗa labarai a Najeriya, ta ci tarar kafofin yaɗa labarai 25 saboda saba ƙa'idar aiki da dokar zaɓe a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na yan majalisun dokoki na tarayya da aka yi a watan da ya wuce. Haka kuma hukumar ta NBC ta yi wa wasu gidajen rediyo 16 gargaɗi na ƙarshe kan laifukan da suka danganci zaɓe. Gidan rediyo 17 ne hukumar ta zarge su da yaɗa abubuwan na siyasa, yayin da ya rage sa'a 24 a yi zaɓe, wanda hakan ya keta doka. Uku daga cikin gidajen rediyon sun fuskanci tuhumar sanya abubuwa na neman haddasa rikici, yayin da hukumar ta tuhumi hudu daga cikinsa da laifin neman raba kai na kabilanci da addini. An ci tarar tasha ɗaya bisa laifin bayyana sakamakon zaɓe tun kafin hukumar zaɓe ta sanar. A wata sanarwa shugaban hukumar ta NBC, Balarabe Shehu Illela, ya buƙaci gidajen talabijin da rediyo da su tabbatar da sun kiyaye da dokokin aikinsu da kuma na zaɓe kafin zaɓen da za a yi ranar Asabar na gwamnoni da 'yan majalisun jihohi a N

Ƙungiyar ƴan a-waren Biafra, IPOB ce ta goma a duniya a ta'addanci - Rahoto

Haramtacciyar ƙungiyar ƴan a-ware ta Biafra, (IPOB) da ke kudancin Najeriya ta zama ta goma a cikin ƙungiyoyin da suka fi aikata ta'addanci a duniya. Wata ƙididdiga da rahoto (Global Terrorism Index (GTI) na wannan shekara ta 2023 da aka fitar na duniya game da ta'addanci wanda ya sanya ƙungiyar a wannan mataki, ya ce hare-hare 40 da kisan gilla 57 da ta aikata a 2022 su suka sa ta kai wannan mataki. Daga cikin kisan gillar da IPOB din ta aikata akwai na hallaka wasu sojojin Najeriya ango da amarya, wadanda ta gille musu kai, da kisan 'yan arewacin kasar da ke kudu maso gabashi da kuma kisan jami'an tsaro da dama. Rahoton wanda ya bayyana ƙungiyar ta IPOB da cewa mai haɗarin gaske ce a ta'addanci, ya sanya Al-Shabaab a matsayin ta ɗaya a duniya wajen ta'addanci. Ƙungiyar ta Al-Shabaab wadda take da ƙarfi a gabashin Afirka rahoton ya nuna cewa ta yi kisan gilla 784 da hare-hare 315, yayin da ƙungiyar IS ta lardin Khorasan (ISK) ta yi kisa 498 da kuma hare-h

Sheikh Shuraim ya yi ban-kwana da limancin Masallacin Makkah

A yanzu dai ta tabbata cewa Sheikh Saud Ash Shuraim ya bar limanci a Masallacin Ka'abah bayan da hukumar da ke kula da manyan masallatai biyu mafiya tsarki na duniya wato masallacin Makka da kuma na Madina ta fitar da jerin sunayen limaman da za su jagoranci sallar Tarawi, kuma ba sunanshi. Tun a watan Janairu rahotanni suka bayyana cewa wani daga cikin fitattun limaman ɗaya daga cikin manyan masallatan biyu ya bar aikin. Amma kuma sai a watan jiya na Fabarairu ta bayyana cewa limamin da zai yi ritayar shi ne Sheikh Saud Ash Shuraim. Sai dai ba a bayyana dalilan da suka sa lilamin ya yi ritaya haka da wuri ba, amma kuma wasu kafofi sun nuna cewa shi da kansa ya buƙaci barin limancin. Limamin wanda ya shafe shekara 32 yana jagorantar sallah, ya ja sallarsa ta ƙarshe a masallacin na Ka'abah ranar Litinin 12 ga watan Rabi Al Awwal 1443 ( Litinin 18 ga watan Oktoba 2021).

Juma'a 17/3/2023

Zakuna sun kashe shugabansu bayan sun yi masa tawaye

Dandazon ma’aikata da masu ziyarar yawon buɗe ido a wani lambun shakatawa na cigaba da bayyana alhininsu bisa tsautsayin da ya fada wa wani shahararren zaki Bob Junior, wanda aka fi sani da suna Snyggve a shafukan intanet. Zakin mai saukin hali, wanda hotunansa ke ɗaukar hankali a shafukan sada zumunta, na da matukar kima a idon abokan hamayyarsa, ya kuma shugabancin namun dawan da ke dajin Serengeti na ƙasar Tanzaniya. Inda ya shafe tsawon shekara bakwai yana zuba mulki a dajin tare da taimakon ɗan uwansa mai suna Tryggve. Ana fargabar wasu ƙananan abokan hamayyarsa ne suka kashe shi. Fredy Shirima, jami’i mai kula da gandun dajin na Serengeti, ya tabbatarwa da BBC faruwar lamarin. Ya ce “yawancin irin wannan al’amari yana faruwa ne a lokacin da shugaban dawa da ke mulki ya tsufa, ko kuma a wasu lokuta, idan mazajen zakuna ba sa farin ciki da yadda ake tafiyar da gandun dajin," a cewar jami’in. "Ana fargabar shima ɗan uwan nasa ya gamu da ajalinsa, sai dai muna ƙoƙa

NDLEA ta kama basaraken gargajiya da laifin safarar ƙwaya

Hukumar da ke Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce jami'antsa sun kama wani Basaraken gargajiya da tubabben ɗan Boko Haram da wasu mutum 35 bisa laifin safarar muggan ƙwayoyi. A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta Twitter mai ɗauke da sa hannun jami'in hulda da jama'a na hukumar Femi Babafemi, ta ce ta samu nasarar kama muggan ƙayoyin a cikin na'urar daskarar da abubuwa ta 'firinji' da kuma tukwanen gas a filin jirgin sama na Legas da ke kudu maso yammacin ƙasar. Sanarwar ta ƙara da cewa jami'an hukumar sun kuma lalata gonakin da ake noma tabar wiwi da girmansu ya kai hekta 39.8 a jihohin Edo da Ondo. Basaraken gargajiyar mai suna Baale Akinola Adebayo - sarkin Kajola, garin da ke kan iyakar jihohin Edo da Ondo - na daga cikin mutum 27 da hukumar ta ce ta kama da laifin safarar ƙwayoyin da nauyinsu ya kai tan 2.2 a faɗin jihohin ƙasar 12 cikin makon da ya gabata. Haka kuma hukumar ta ce ta kama Alayi Modu - wanda ya ƙw

DEEJARH BERVER ENTERPRISES

DAMA GARE KU MATA!!! DAMA GARE KU MATA MASU BUKATAR KOYON GIRKE-GIRKEN KWALAM DA MAKULASHE, KUNA ZAUNE TSAF DAGA CIKIN GIDAJENKU. DEEJARH BERVER TA SHIRYA TSAF DOMIN KOYO MUKU HADADDUN GIRKE-GIRKE, YADDA ZAKI SARRAFA ABINCI DA LEMOKA DA HADIN SALAD DA SNACKS HAR GUDA 40, TAMKAR KUNA GABANTA. ZA A GABATAR DA KOYARWAR TA CIKIN WAYOYIN HANNUNKU WATO TSARIN ONLINE LECTURE MAI DAUKE DA HOTON VIDEO DA RUBUTU DALLA-DALLA AKAN TA CIKIN MANHAJAR WHATSAPP DA TELEGRAM. KOWA NA DA DAMAR YIN TAMBAYA KO TATTAUNAWA DA MALAMA A SIRRANCE. KU DAI KU YI RIJISTA A YAU AKAN KUDI NAIRA 2,500 KACAL. ZA MU FARA KOYARWA RANAR 18 March, 202. DOMIN KARIN BAYANI KIRA WANNAN LAMBAR 09079274454

INEC Ta Dage Zaben Gwamna Da ‘Yan Majalisun Jiha

An bayyana cewa, dage zaben ya biyo bayan gazawar hukumar ta sake fasalin na’urorin tantance masu kada kuri’a (BVAS) da aka yi amfani da su a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, domin samun damar yin amfani da su a zaben jihar. Majiya mai tushe ta shaida wa Taskar Lafazi cewa hukumar gudanarwar hukumar na gudanar da wani taro a halin yanzu, inda ta ke nazarin ko dai ranar 18 ga watan Maris ko 25 ga watan Maris domin gudanar da zaben. Sai dai an samu labarin cewa an zabi ranar 18 ga Maris. An kuma bayyana cewa sake fasalin BVAS zai dauki kwanaki uku ko hudu kuma tunda duk za a kai su hedkwatar Abuja, za a sake gyara injinan a kai su jihohi daban-daban daga karshe zuwa rumfunan zabe.

Juma'a 10/3/2023