Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya. Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce ganin jinjirin watan da aka yi a a kasar ya sanya ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1444. Kwamitin tantance ganin wata karkashin jagorancin Maigirma Wazirin Sakkwato Farfesa. Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan a bana. Cikin sanarwar da ya yi Sarkin Musulmi ya ce "mun samu bayanai daga wurare daban-daban a Najeriya kuma mun zauna da masana domin tabbatar da ingancin waɗannan bayanan gabanin mu sanar da al'umma cewa an ga watan. Domin haka gobe Juma'a 21 ga watan Afrilu 2023 ita ce 1 ga watan Shawwal 1444," in ji Sarkin Musulmi. Ya yi kira ga sauran musulmin ƙasar da su ajiye azumi domin an ga wata, su kuma yi shirin zuwa masallaci domin halartar Sallar Idi a wurare daban-daban. Akasarin Musulmai a fadin duniya dai sun tashi da Azumin watan Ramadan ra
Shafin yanar gizo na mujallarku mai farin jini, wato Taskar LAFAZI.