Shugaban hukumar sauraron ƙorafe-ƙorafen al'umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano watau PCACC, Barista Muhuyi Magaji ya ce zai gudanar da wasu jerin bincike a kan tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da gwamnatinsa. Daya daga cikin binciken da shugaban na yaki da rashawa a Kano yace zai mayar da hankali a kai shi ne binciken 'bidiyon dala'. A ranar Laraba ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da mayar da Barista Muhuyi kan muƙaminsa nasa, bayan korarsa da tsohuwar gwamnatin jihar ta yi bisa dalilin cewa akwai shakku kan yanayin tafiyar da ayyukansa. Sai dai kwana ɗaya bayan mayar da shi kan muƙamin, shugaban na PCACC ya shaida wa BBC cewar akwai wasu jerin zarge-zarge a kan gwamnatin Ganduje, waɗanda yake shirin buɗe bincike a kansu. Ya ce "Za mu ɗora daga inda muka tsaya, dama akwai wasu bincike-bincike da muke yi wadanda daga baya wasu suke ganin ba za su yadda a ci gaba da yi ba saboda ya shafe su." Lamarin ya fara tay